Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen, Thomas Tuchel, ya bayyana cewa har yanzu wasa bai kare ba a haduwar su da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City a gasar cin kofin zakarun Turai na bana.
A ranar Talata ne Manchester City ta doke Bayern Munich da ci 3-0 a wasan farko zagayen kuarter finals a Champions League da suka kara ranar Talata a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester.
- Masanin Tattalin Arziki: Kasar Sin Ce Karfin Ci Gaban Tattalin Arzikin Duniya
- Sallah: Gwamna Bagudu Ya Umarci A Biya Albashin Watan Afrilu
Minti 27 da fara wasa Manchester City ta ci kwallon ta hannun Rodrigo Hernandez, bayan da suka koma zagaye na biyu Bernardo Silba ya kara ta biyu, Erling Haaland ya ci ta uku minti bakwai tsakani.
Kuma kwallo ta 45 da Haaland ya ci a bana a dukkan fafatawa, ba wani dan wasan dake buga Premier mai wannan bajintar kuma wasa na bakwai da suka kara a Champions League a tsakaninsu, Manchester City ta ci hudu, Bayern ta yi nasara a uku.
”Duk da cewa mun yi rashin nasara hakan ba zai sanyaya mana gwiwa ba saboda akwai ragowar wasa nan gaba kuma naji na kara kaunar ‘yan wasa na saboda yadda suka buga wasa mai kyau.”
Manchester City ta kawo wannan matakin bayan da ta fitar da RB Leipzig, ita kuwa Bayern ita ce ta yi waje da Paris St Germain, sannan wannan shi ne karon farko da suka kara a kuarter finals, bayan da sauran fafatawar da suka yi a cikin rukuni suka yi.
Wannan shi ne karo na 21 da Bayern ta kai wasan kusa da kusa da na karshe a kofin zakarun Turai, wadda ta dara Real Madrid mai 19 kuma Manchester City ce kadai cikin masu kai wa zagayen dab da na kusa da na karshe a kaka shida a jere a baya.
Wasa na karshe tsakanin Manchester City da Bayern shi ne na 2014, wanda kungiyar Ingila ta yi nasara a gida da cin 3-2 kuma kowacce ta ci uku-uku, wannan shi ne wasan farko da za su kece raini a zagayen kuarter finals, a cikin rukuni suka kara a baya a fafatawa shida.
Wasa shida tsakanin Man City da Bayern Munich
kofin zakarun Turai Talata 25 ga watan Nuwambar 2014. Man City 3 – 2 B kofin zakarun Turai Laraba 17 ga watan Satumbar 2014. B Munich 1 – 0 Man City. kofin zakarun Turai Tu 10Dec 2013. B Munich 2 – 3 Man City. kofin zakarun Turai 02Oct 2013. Man City 1 – 3 B Munich. kofin zakarun Turai 07Dec 2011. Man City 2 – 0 B Munich. Kofin Zakarun Turai Tu 27Sep 2011. B Munich 2 – 0 Man City. Bayern Munchen ta kai zagayen gaba a wasa biyar daga shida da ta fuskanci kungiyoyin Ingila a ziri daya kwalle, in ban da kakar 2018/19 a zagaye na biyu da Liberpool.
Bayern ta ci wasa hudu a jere a kan kungiyoyin Premier League, wasan farko da aka doke ta a karawa biyar da ta kai ziyara Ingila, wadda ta ci uku da canjaras daya. Sai dai Manchester City ta ci wasa na 11 a jere a gida a kan kungiyoyin Jamus a Champions League da cin kwallo 42 kuma aka zura mata guda 10.
Ranar Laraba 19 ga watan Afirilu, Bayern Munich za ta karbi bakuncin kungiyar Manchester City a wasa na biyu a Kofin Zakarun Turai zagayen kuarter finals a filin wasa na Allianz Arena.