Asabar din nan ne, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin JKS Wang Yi ya gana da ministar harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock a nan birnin Beijing.
A yayin ganawar, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba manufar harkokin waje mai cin gashin kanta, da tabbatar da bin dabarun bude kofa na samun moriyar juna da cimma nasara tare, da kiyaye ikon MDD da tsarin kasa da kasa da aka kafa bayan yakin duniya na biyu. Wang Yi ya kara bayyana cewa, kasar Sin na son karfafa cudanya da mu’amala da kasar Jamus domin inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata.
A nata bangare, Baerbock ta ce, kasancewar kasar Sin mambar dindindin a kwamitin sulhu na MDD, kuma kasar Jamus babbar kasa a nahiyar Turai, yana da matukar muhimmanci ga bangarorin biyu su karfafa tattaunawa da mu’amala. Kuma kasarta na martaba manufar Sin daya tak a duniya.
Baya ga haka, a jiya ne, ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya gudanar da taron tattaunawa kan harkokin diplomasiyya da tsaro karo na shida tsakanin kasar Sin da Jamus tare da takwararsa ta kasar ta Jamus Baerbock a nan birnin Beijing.
A yayin taron, Qin Gang ya ce, kasashen Sin da Jamus abokan hadin gwiwa ne ba abokan gaba ba, kuma ya kamata sassan biyu su bunkasa dangantakarsu da kansu. Kasar Sin tana son yin mu’amala da kasar Jamus tare da inganta hadin gwiwa a dukkan fannoni.
A nata bangare, Baerbock ta bayyana cewa, kasar Jamus na ci gaba da raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin cikin ‘yanci, kuma tana fatan dawo da mu’amala da tattaunawa a fannoni daban-daban a tsakanin kasashen biyu cikin sauri. Ban da wannan kuma, bangaren Jamus yana mai da hankali sosai kan kiyaye tsarin samar da kayayyaki, bai amince da “mayar da wani bangare saniyar ware a fannin tattalin arziki” ba, kuma yana tsayawa tsayin dak kan nuna daidaito ga kamfanonin juna. (Mai fassara: Bilkisu Xin)