• English
  • Business News
Tuesday, October 14, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sana’ar Su

by Leadership Hausa
2 years ago
Su

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa a wannan shafi namu mai albarka. Yau za mu yi magana akan yadda ake sana’ar kamun kifi wato ‘Su’.

Sana’ar Su ita ce sana’ar kamun kifi da sauran halittun cikin ruwa. Sana’a ce mai dimbin albarka kuma sana’a ce dadaddiya wacce akan shiga ruwa ko dai kai tsaye a yi amfani da hannu ko kuma ta hanyar amfani da wani abu domin kama kifi a ciki ko a sayar. Wannan sana’a ta kamun kifi tana daga cikin dadaddun sana’o’in kasar Hausa.

  • Wang Yi Da Qin Gang Sun Gana Da Ministar Harkokin Wajen Jamus 
  • Alhassan Ado Doguwa Ya Sake Lashe Zaben Dan Majalisar Wakilai A Kano

Mai yin wannan sana’a ana kiran shi da suna masunci. Ana gudanar da sana’ar kamun kifi a cikin kogi, tafki, korama, gulbi, injari da sauran wuraren wucewa da kuma taruwar ruwa.

Tasirin da sana’ar Su take da shi a kasar Hausa ya sanya su ma suna da sarkin ruwa. Sannan kuma suna bukukuwa irin nasu. Masunta kan jefa ‘ya’yansu a cikin ruwa su yi kwana da kwanaki a ciki ba tare da sun ciro su ba.

Kayan aiki

LABARAI MASU NASABA

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

  1. Kugiya: Ana kafa ta a cikin ruwa a lankaya wani abu da kifi zai ci a jikinta, sai a baza ta a cikin wani yanki na ruwan da ake son kama kifi a ciki.
  2. Mali: Abu ne da ake yinsa da ita ce da raga ta zare. Ana tsoma shi cikin ruwa idan kifaye suka shiga ciki sai a fito da shi a kwashe.
  3. Kalli: Shi kuma raga ce ta zare ake kafewa a cikin ruwa, sai a ja ta zuwa wani gefen, idan kifaye suka taru a ciki sai a fito da su a adana.
  4. Birgi: Raga ce ta zare, wacce ake cin bakinta da dalma. shi kuma birgi watsa shi ake yi a cikin ruwa, sai dalmar ta shiga ciki baya iya fita, idan suka shiga ciki suka taru, sai a janye shi zuwa gabar ruwa a firfito da su a adana.
  5. Fatsa: Ita cards kugiya ce guda daya ko biyu ake daurawa a jikin sanda, sai a lankaya wani abincin da aka san kifi yana so, da zarar ya hadiyi wannan abincin, sai kukiyar nan ta makale masa a wuya, sai a fizgo da karfi a wullo shi wajen ruwa a kama.
  6. Dalla: ita ma raga ce ta zare, wacce ake rike gefe da gefenta, sai mutane su ratsa cikin ruwan suna ja. duk kifi da suka tokare shi to ba zai iya wucewa ba. Can zuwa wani lokacin sai su nannade ta da kifaye a ciki su fita da ita wajen ruwa sai su ciccire kifin.
  7. Koma: Ita koma jaka ce ta raga da ake yi wa katon baki. ridi biyu ake yin ta, ana rike kowacce daya kuma a hagu, idan aka shiga ruwa da ita sai a rika tafiya, can kuma sai a hade bakin a fitar waje.
  8. Gora: Gora hawa kanta ake yi ana iyo a cikin ruwa domin zuwa gurin da aka kafa mali, birgi ko makamantansu.
  9. Kwale-kwale: Abin sufuri ne na cikin ruwa. Da fatan wannan zai taimaka gun kamun kifi da sauran abubuwan ruwa. Allah ya ba da sa’a.
ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC
Sana'a Sa'a

Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC

August 3, 2025
Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera
Sana'a Sa'a

Sana’ar Hada Sabulun Aloe Vera

February 1, 2025
Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
Labarai

Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi

November 22, 2024
Next Post
Ra’ayoyinku A Kan Cece-kucen Shirin Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya

Ra’ayoyinku A Kan Cece-kucen Shirin Kafa Gwamnatin Rikon Kwarya

LABARAI MASU NASABA

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

Xi Jinping Ya Gana Da Shugaban Ghana Da Firaministar Mozambique

October 14, 2025
‘Yan Majalisa 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga PDP

PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai

October 14, 2025
An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

An Kashe Mutum 3, Wasu 7 Sun Jikkata Sakamakon Ɓarkewar Rikici A Jihar Jigawa

October 14, 2025
Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

Rashin Tsaro A Nijeriya Ba Zai Ƙare Ba Matuƙar Ba A Samar da Ayyukan Yi Da Mulki Na Adalci Ba – Amaechi

October 14, 2025
Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

Amnesty International Ta Soki Tinubu Kan Yi Wa Masu Laifin Take Haƙƙin Ɗan Adam Afuwa

October 14, 2025
‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Jarida A Kan Hanyarsa Ta Zuwa Ɗaukar Horo A Kwara

October 14, 2025
Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

Zaman Gidan Yari Ya Nuna Min Mutanen Da Ya Kamata Na Yi Hulɗar Siyasa Da Su — Faruk Lawan

October 14, 2025
Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

Majalisa Na Shirin Sauya Lokacin Zaɓen 2027 Zuwa Nuwamba 2026

October 13, 2025
Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

Yajin Aiki: Malaman Jami’a Sun Ce Barazanar ‘Ba Aiki, Ba Biya’ Ba Zata Tsorata Su Ba

October 13, 2025
Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

Nazarin CGTN: Jama’ar Duniya Sun Jinjinawa Rawar Da Mata Ke Takawa A Harkokin Ci Gaba

October 13, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.