Wani kare a kasar Portugal ya zama wanda ya fi ko wanne kare shekaru a tarihin duniya, ya karta tarihin da aka shafe sama da shekara 100 da kafawa in ji – Guinness World Records.
Bobi na cikin jinsin karnukan Rafeiro do Alentejo – da a rayuwa ba sa wuce shekara 12 zuwa 14.
- Shawarar Kasar Sin Game Da Tsaron Kasa Da Kasa Ta Ingiza Zaman Lafiya Da Daidaito A Duniya, In Ji Masana
- Abin Da Ya Zama Wajibi Manoman Rogo Su Yi Don Samun Amfani Mai Yawa
Karen da a baya yake rike da wannan tarihi shi ne Bluey da ke Australia, wanda ya mutu a 1939 yana da shekaru 29 da wata biyar a raye.
Ranar 1 gawatan Fabirairu Bobi ya cika shekara 30 da kwana 226, kuma yana yin abin duk da ake so a wannan shekarun nasa.
An tabbatar da shekarun nasa ne ta hannun gwamnatin Portugal karkashin kulawar Hukumar Kula da Dabbobi ta kasar, kamar yadda Guinness World Records ta bayyana.
Ya na zaune da iyalan Costa a kayen Conkueiros a duk tsayin rayuwarsa, da suke zaune a gabar tekun Portugal, kuma yana da ‘yan uwa uku da mahaifiyarsa ta haifa.
Leonel Costa, wanda shekararsa takwas a lokacin, yace mahaifansa na da dabbobin da suke kiwo da dama, don haka suka yasar da wasu da yawa sai dai Bobi ya tsallake rijiya da baya.
Leonel da dan uwansa sun rika boye Bobi suna ci gaba da kiwonsa, har sai lokacin da ya zama wani bangare na gidansu, wanda yake ba shi abinci irin wanda suke ci.
“Tsakanin abincin gwangwani na dabbobi da nama, Bobi bai fiye damuwa ya ci ko daya ba, ya fi damuwa ya ci irin abin da muke ci, in ji Mista Costa, wanda ko da yaushe yake neman abincinsa cikin ruwa.
Bayan wata rashin lafiya da ya yi a 2018 har aka kwantar da shi a asibiti saboda gaza numfashi da ya yi, Mista Costa ya ce kare na rayuwa ne cikin kwanciyar hankali, kuma sirrin tsayin rayuwarsa shi ne “nutsuwa da samun muhallin da ke cike da zaman lafiya” da yake rayuwa cikinsa.
Kuma kamar gado ya yi daga wajen mahaifiyarsa, mahaifiyar Bobi sai da ta yi shekara 18 a raye.
Amma duk da haka, lokaci na neman cimma Bobi, domin yanzu yana da matsalar kafa da kuma gani.
Costa ya ce Bobi shi ne “na karshe a tsarin dabbobin” a gidanmu kuma ya ce “shi din na daban ne.”
Nadin da aka yi wa Bobi na karen da ya fi dadewa a duniya na zuwa ne mako biyu bayan Guinness World Records ta nada wani kare Spike the Chihuahua, mafi dadewa a raye wanda ya kwashe shekara 23 a raye.
Amma bayan nan sai kungiyar ta sauya tarihin ta sanar da Bobi a matsayin karen da ya fi dadewa a duniya.