Daurarru fiye da 3200 ne a gidajen yarin Nijeriya ke jiran a zartar musu hukuncin kisa, kamar yadda hukumar kula da gidajen gyaran hali ta Nijeriya ta bayyana.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya ambato mai magana da yawun hukumar Abubakar Umar yana cewa ba ko yaushe, ake zartar da hukuncin kisa nan take da zarar kotu ta yanke hukunci ba.
- Ko Kanawa Za Su Yafe Wa Ganduje?
- Nijeriya Ta Sanya Hannu A Yarjejeniyar Amfani Da Fasahar Shuka Itatuwa Da Kasar Netherlands
Ya ce sau da yawa, fursunonin da aka yanke wa hukuncin kisa kan shafe tsawon lokaci a halin rashin tabbas, daidai lokacin da ake daukaka kararraki.
A watan Yulin bara, jaridar Punch ta ambato hukumar kula da gidajen yarin Nijeriya na cewa adadin wadanda ke zaman jiran a zartar musu da hukuncin kisa ya kai 3,145.
Hakan dai na nufin a cikin wata tara kawai, mutum 153 kotuna suka sake yanke wa hukuncin kisa a Nijeriya.
Wani rahoton Amnesty International na 2021, ya sanya Nijeriya a matsayin ta uku a duniya cikin jerin kasashen masu yawan daurarru da ke jiran a kashe su.
Mai magana da yawun hukumar gidajen yarin Nijeriya ya ce “Daurarrun da ke zaman jiran kisa na rayuwa ne a bangarensu daban, yayin da wasu kan kwashe fiye da shekara 15 suna jiran a zartar musu da hukunci, bayan kotu ta yanke shari’a.
A cewarsa mutum 3,298 ne suke jiran hauni ya aiwatar da hukuncin da aka yanke musu bayan kotuna sun same su da laifi.
Ya kuma ce adadin masu jiran a zartar musu da hukuncin kisan ya kai kashi 4.5 na illahirin daurarrun da ke tsare a kasar.
Abubakar Umar ya kara da cewa ana daure da wasu masu zaman jiran a zartar musu hukuncin kisa tun lokacin da aka kama su, har zuwa lokacin da ake yi musu shari’a, kafin a yanke musu hukunci.
Ya ce da yawan mutanen sun aikata laifuka ne kamar kisan kai da fashi da ta’addanci da sauransu.