Mamakon ruwan sama ya shanye gidaje da dama a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba a safiyar ranar Litinin.
Leadership Hausa ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a lokacin da kogin Mayo Gwoi ya malalo bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka dauki tsawon sa’o’i biyu ana tafkawa.
- Basarake Ya Mutu A Hannun ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Shi A Kogi
- Za Mu Tabbatar An Kwaso Daliban Da Suka Makale A Sudan -Gwamnatin Tarayya
Gidajen da ambaliyar ta shafa suna kusa da gabar kogin.
Duk da cewa ba a samu asarar rayuka ba, amma ambaliyar ta lalata dukiya da suka hada da kayan gida da kuma kayayyakin abinci na miliyoyin Naira.
Ruwan saman dai kusan shi ne na farko-farko tun bayan da daminar bana ta fadi a yankunan Arewa.