Jami’ar Bayero da ke Kano ta sanar da rasuwar magatakardanta, Malam Jamil Ahmad Salim da safiyar yau Laraba.
Tun da farko an wallafa sanarwar ne a shafin Facebook na Jami’ar ta BUK, inda aka sanar da al’ummar Musulmi waje da lokacin da za a yi jana’izar marigayin.
Sanarwar ta ce za a yi jana’izar mamacin da misalin karfe 10 na safe a babban Masallacin Juma’a da ke sabuwar Jami’ar da ke kan titin zuwa Gwarzo a birnin Kano.
Talla
Tuni dai aka yi jana’izar tasa kamar yadda sanarwa ta gabata.
‘Yan uwa da abokan arziki da daliban malamin sun shiga bayyana alhininsu kan rasuwarsa a shafukan sada zumunta.
Talla