Sakamakon irin ɓarnar da yaɗa labarun ƙanzon kurege ke yi a cikin jama’a, an jaddda buƙatar tabbatar da hukunci ga duk wanda aka kama da hannu wajen yaɗa ire-iren waɗannan labarun.
Wani babban jami’in shige da fice mai muƙamin Kwanturola, CI Sunday James ya yi kiran a wata muƙala da ya rubuta.
Sunday James ya bayyana cewa, ci gaban da ake samu na amfani da kayan zamani wajen sadarwa na ƙara samar da fagen da masu yaɗa labarun ƙanzon kurege ke cin karensu ba babbaka.
“Abin da ake nufi da labarin ƙanzon kurege shi ne, duk wani labari mara tushe balle asali da aka kitsa aka yaɗa ta hanyar jita-jita daga wani mutum ko gungun wasu mutane. Sukan yi amfani da fasahohin zamani na sadarwa su ƙirƙiri labari da zai yi kama da na gaskiya tare da wallafawa a wuraren da suka san jama’a za su gani domin haifar da ruɗani da kawar da hankulan jama’a daga labarai na gaskiya don su cimma mummunan ƙudirinsu na tayar da husuma ko shafa wa wanda suke nufi kashin kaji.”
Jami’in ya ci gaba da cewa, labarai na ƙarairayi ba su haifar da ɗa mai ido a cikin al’umma, saboda ana yi ne domin s ci mutuncin wani da ɓata masa suna ta yadda zai zama abun ƙyama a cikin jama’a. “Shi ya sa idan har aka yi wa mutum, bayar da haƙuri da neman yafiya ba su iya goge ɓarnar da labarun ƙanzon kurege suka yi wa mutum.
“Don haka ‘yan jarida, marubuta da sauran masu hannu a sha’anin sadarwa su yi kaffa-kaffa tare da tantance sahihancin duk wani labari da za su yaɗa kafin su kai ga fitarwa ga jama’a.” In ji CI Sunday James.
Sunday James dai shi ne tsohon jami’in hulɗa da jama’a na Hukumar Kula Da Shige Da Fice ta Ƙasa kafin a ƙara masa girma zuwa muƙamin Kwanturola a hukumar.