ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Batun Tuhumar Ƙananan Yara Da Laifin Shirya Juyin Mulki

by Ra'ayinmu
2 years ago
Yara

A kwanakin baya ne, kafafen yada labarai na cikin  gida da na kasashen waje suka kasance cike da labaran gurfanar da kananan yara da babbar kotun tarayya ta yanke masu hukuncin cin manar kasa saboda gudanar da zanga-zangar kawo karshen rashin gudanar da shugabanci na gari a Nijeriya da kuma sauran aikata laifuka.

Wani babban abin takaici shi ne, yadda kafafen yada labarai na kasashen waje suka wallafa cewar, gwamnatin kasar nan, za ta yankewa su yaran 29 hukuncin kisa saboda gudanar da halin yunwar da aka shiga a kasa.

  • Gwamnatin Kano Ta Miƙa Yara 76 Da Aka Kama Yayin Zanga-zangar Tsadar Rayuwa
  • Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Ƙaddamar Da Biyan Bashin Waɗanda Aka Tsare A Gidan Gyaran Hali

Sai dai kuma, wasu kwararrun Lauyioyi da kungiyoyin kare rajin ‘yancin ‘yan Adam a kasar, sun fito karara sun yi tir da kama yaran da mahukuntar kasar suka yi kan gudanar da zanga-zangar, musamman ma idan aka yi la’akari da yadda wasu daga cikin yaran da aka gurfanar a gaban babbar kotun tarayya bayan an gurfanar da su a gaban kotun domin bukatar bayar da belinsu.

ADVERTISEMENT

Kazalika ma, lamarin ya kuma kara yamutsewa hakan ya biyo bayan zargin da aka yi na cewa, a lokacin da suke tsare a hannun ‘yan sanda, sun ci zarafin su, wadanda kuma ‘yan sandan suka mayar da su tamkar wadanda suka aikata wani babban laifi.

Makomar wadannan yaran dai, tasa tunawa da zanga-zangar #EndSARS wadda wasu jami’an tsaro suka yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin masu zanga-zangar a lokacin da suke kan yin zanga-zangar.

LABARAI MASU NASABA

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

Me yiyuwa sukar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sha ne, ya tilasata shi bayar da umarni nan take, da a saki yaran a kuma gaggauta mika su ga iyayensu.

A nan, muna jinjinawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ceto rayuwar yaran daga hannun jami’an tsaron, musamman ma  idan aka yi la’akari da irin wahalar da suka sha a hannun ‘yansanda.

A bisa tunanin, tun da farko bai kamata ma ace ‘yan sandan sun kama yaran ba, domin yaran dai, sun yi zanga-zangar ce kan kuncin rayuwa.

Zaman da yaran suka yi a kulle, hakan ya nuna cewa, an barsu ne a cikin yunwa da kasancewa a cikin rashin lafiya don kawai sun gudanar da zanga-zangar fargar da gwamnati kan ci gaba da kasancewar talakawan kasar, a cikin kangin talauci.

Kwanci tashi, irin juyin juya hali da ya auku a kasar Faransa, ya janyo kifar da masarautar garjiya ta kasar, musamman ma, ba wai don samun yawan talauci ba, amma saboda irin mulkin gurguzu da masarautar ke yiwa ‘yan kasar.

Kazalika ma, kasar Rasha ba wai an kifar da gwamnatin kasar ne da makamin kari dangi ne ba, abin ya kawo karshen shugabannin  kasar ba, amma boren da ‘yan kasar suka gudanar ne, ya kawo karshen shugabancin mahukuntar kasar, ya biyo bayan jefa rayuwarsu a cikin kangin rikcewar rayuwa.

Namu ra’ayin a nan shi ne, akasarin kasashe ba su koyon darasi a kan kuskuren da wasu kasashen suke tabkawa.

Abinda ke faruwa a Nijeriya shi ne, kusan matakan da bangaren gwamnatoci uku na kasar ke yi, ba su daukar kwararan matakan da suka dace.

Duk kasar da ta kasance kayan abinci da sauran kayan amfanin yau da kullum sun fi karfin talakan kasar, amma masu rike da madabun iko na siyasa, suna yin wandaka da watanda da kudaden gwamnati yadda suke so, suna kuma barin ‘ya’yan talakawa a cikin kangin halin yunwa, wannan babban abin bakin ciki ne.

Ra’ayinmu a nan irin yadda yaran suka tsinci kansu a cikin cin zarafin gwamnatin su, wadda ya kamata ta nuna cewa, mulkin dimokiradiyya ne ake gudanarwa a kasar hakan kuma ya nuna cewa, tamkar ana gudanar da mulkin mallakar Fir’aunanci ne a kasar.

A matsayin a wannan jaridar, mun nuna taikaicin mu a kan irin halin da yaran suka tsinci kansu a lokacin da aka tsare su, wanda kuma jami’an tsaro suka dauke su tamkar wasu masu mugun hadari a cikin alumma.

A bisa tunanin mu, irin wannan halin da aka jefa yaran a ciki, hakan zai iya juya tunanin su zuwa rungumar munanan dabi’u.

Ya zama wajbi mu ankarar da mahukunta don su gane cewa, ya kamata su san yadda za su rinka tafiyar da yara a duk lokacin gudanar da wata zanga-zanga, kamar dai irin ta #EndBadGobernance.

Yara
Ra'ayinmu
+ postsBio
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Kisan Gillar Marabar Jos: Bai Kamata Jinin Malama Ummulkhairi Ya Tafi A Banza Ba
  • Ra'ayinmu
    https://hausa.leadership.ng/author/raayinmu/
    Shin Nijeriya Ta Shirya Tunkarar Dawowar Annobar Ebola?

MASU ALAKA

Yara
Ra'ayinmu

Batun Shayar Da Jarirai Nonon Uwa Da Ƙalubalen Abinci Mai Gina Jiki

August 14, 2026
Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG
Ra'ayinmu

Buƙatar Kawo Ƙarshen Dogon Layi A Tashoshin Sayen Iskar CNG

July 31, 2026
Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi
Ra'ayinmu

Ana Ci Gaba Da Tafka Muhawara Kan Shirin Gwamnati Na Haramta Masana’atun Sarrafa Robobi

July 10, 2026
Next Post
Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima…

Dambarwar Shirin Tinubu Na Yi Wa Dokar Haraji Kwaskwarima...

LABARAI MASU NASABA

Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.