Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bi sahun sauran shugabannin kasashen duniya domin nadin sarautar Charles III da uwargidansa Camilla a matsayin mai martaba sarki da Sarauniyar Ingila.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba.
- Saboda Ziyarar Tinubu, Wike Ya Ba Da Hutu, Ya Umarci Rufe Kasuwanni
- Ba A Taba Tsareni A Burtaniya Ba, Peter Obi Ya Fayyace Zare Da Abawa
Adesina ya ce shugaban kasar zai tafi birnin Landan na Birtaniya a ranar Laraba domin bikin nadin sarautar da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar 6 ga watan Mayu.
“Kafin nadin sarautar, sakatariyar Commonwealth za ta yi amfani da damar taron shugabannin da za a yi a Landan don karbar bakuncin taron koli na shugabannin gwamnatocin kasashen Commonwealth a ranar Juma’a 5 ga Mayu.
Sanarwar ta kara da cewa “An bukaci shugaba Buhari da ya halarci taron da za a tattauna kan makomar kasashen Commonwealth da kuma rawar da matasa za su taka.”
Shugaban zai samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama; Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Manjo-Janar Babagana Monguno (mai ritaya); Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA), Ambasada Ahmed Abubakar; Shugabar hukumar ‘yan Nijeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa; da sauran manyan jami’an gwamnati.
A watan Nuwamba ne Buhari ya gana da Sarki Charles III a fadar Buckingham domin kulla alaka tsakanin Nijeriya da Birtaniya.
Shugaban kasar ya ce sarkin na yanzu, wanda aka nada sarauta bayan rasuwar mahaifiyarsa, “yana magana da Nijeriya sosai kuma yana son dangantakarsu ta ci gaba.”
Nijeriya, wacce a da ta kasance kasar da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka, ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoba, 1960 a lokacin mulkin Sarauniya Elizabeth ta biyu wadda ta rasu a watan Satumban 2022 tana da shekaru 96.