A yau Juma’a, za a kawo karshen bikin kasuwanci na Canton Fair karo na 133, da ake gudanarwa a birnin Guangzhou na kasar Sin. Yadda aka karya bajintar tarihi a fannonin fadin wurin gudanar da bikin, da yawan kamfanonin kasashe daban daban da suka halarta, ya nuna tasirin bikin Canton Fair, da karfinsa a fannin jan hankalin ‘yan kasuwan sassan duniya.
A fannin baje kolin kayayyakin da ake shigar da su cikin kasuwannin kasar Sin daga ketare, bikin Canton Fair na wannan karo ya nuna wani yanayi mai armashi, inda yawan kamfanonin kasashe da yankuna masu alaka da shirin “Ziri Daya da Hanya Daya” (B&R) wadanda suka halarci baje kolin ya kai 370, kimanin kashi 73% cikin dukkan kamfanonin da suke baje kolin kayayyakin da ake shigar da su cikin kasar Sin.
Hakika, a shekarun baya, bikin Canton Fair ya riga ya zama wani dandali mai mihimmanci ga kasashe da yankuna masu alaka da shirin B&R da suke da niyyar raya hadin gwiwar ciniki tare da kasar Sin. Inda alkaluman da aka samu daga bukukuwan Canton Fair daban daban da aka gudanar da su a baya, suka nuna yadda ake ta samun karuwar ciniki da zuba jari tsakanin kasar Sin da wadannan kasashe da yankuna daban daban. (Bello Wang)