Kungiyar harkokin kasuwanci ta duniya, (EIU), ta bayyana birnin Legas, wanda ya ke babban birnin kasuwanci a Nijeriya, a matsayin birni na biyu mafi munin gudanar da rayuwa a duniya.
EIU ta sanya Legas a matsayi na 171 daga cikin kasashe 172 a cikin jerin biranen da za a iya rayuwa a duniya, a kashin farko na shekarar 2022, bayan sabbin alkaluma da ta fitar.
- Gwamnatin Kano Ta Kafa Kwamitin Da Zai Ke Sanya Ido A Shafukan TikTok Da Instagram
- Ra’ayoyinku A Kan Mataimakin Dan Takarar Shugaban Kasa Na APC Na Wucin-Gadi
Wannan rahoto ya sanya birni mafi kyawu a Najeriya ya zama mafi muni a Afirka yayin da Damascus (Syria) da Tripoli (Libya) ke bin sahun tare da Legas (Najeriya), wanda suke fuskantar tashin hankali na zamantakewa, ta’addanci da rikice-rikice.
“Biranen mafi munin rayuwa su ne Damascus a Siriya, Legas a Najeriya, Tripoli a Libya, Algiers a Aljeriya da Karachi a Pakistan, wadanda suka samu maki 30.7, 32.2, 34.2, 37.0 da 37.5.
“EIU ta kara bayyana manyan biranen duniya guda biyar da suka fi dadin rayuwa a duniya wadanda suka hada da Vienna, Ostiriya wanda ya samu maki 99. 1; Copenhagen, Denmark sun samu 98.0; Zurich, Switzerland na da maki 96.3; Calgary, Kanada na da 96.3, Vancouver 96.1.
“Duk da haka, yawancin biranen da ke cikin kasa goma sun inganta kimarsu idan aka kwatanta da bara, kamar yadda cutar ta COVID-19 ta haifar da matsin lamba,” in ji EIU.
EIU, ta sanya birane 173 a duniya kan abubuwa daban-daban, ciki har da kiwon lafiya, yawan laifuka, kwanciyar hankali, siyasa da kayayyakin more rayuwa d.
EIU na nazarin ingancin kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, kwanciyar hankali, da al’adu lokacin da ake tantance yanayin rayuwa na kowane birni.
Fiye da abubuwa 30 aka yi la’akari da su yayin kididdigar kowane matsayi, wanda sai aka hada su zuwa ma’aunin nauyi tsakanin daya zuwa 100.
Daga alamomin da aka yi amfani da su wajen kididdigar sun hada kwanciyar hankali, kiwon lafiya, al’adu, muhalli, ilimi da ababen more rayuwa, Legas ta samu maki 20.0, 20.8, 44.9, 25.0 da 46.4, wanda yasa ta samu maki 32.2 daga jimillar maki 100.