Wata kotun daukaka kara, ta yi watsi da karar da Shugaba Muhammadu Buhari da Babban lauyan gwamnati suka shigar, kan bukatar fashin baki kan sashe na 84 na dokar zabe ta 2022 da aka yi wa kwaskwarima.
Sashen ya haramata wa duk wani mai rike da mukami na siyasa da aka nada a dukkan matakai ya kada kuri’a a zaben fidda gwani na kowace jam’iyya.
- Peter Obi Ya Jajantawa Ekweremadu Kan Cafke Shi Da Aka Yi a Burtaniya
- Daminar Bana: Manoma A Nijerya Na Cikin Fargabar Ambaliyar Ruwa
Alkalan kotun bakwai da suka yi zamansu a ranar Juma’a a karkashin jagorancin mai shari’a Musa Dattijo, dukansu sun amince cewa karar yunkurin wahalar da kotu ne kawai.
A hukuncin da mai shari’a Akomaye Agi, ya karanto, kotun kolin ta ce ba zai yiwu shugaba Buhari ya nemi a goge sashen na 84 da dokar zabe 2022, wanda a baya ya aminta da shi.
”Shugaban kasa ba shi da ikon bukatar majalisa ko tursasa ta ta sauya wani abu a dokar da a baya ya bada hadin kai ya kuma aminta da shi,” kamar yadda ya bayyana.
Karar ta biyo bayan hukuncin da wata kotu a birnin Umuahia n Jihar Abia, wadda ta soke sashe na 84 (12) karamin sashe na 122.