Gwamnatin Tarayya za ta dakatar da ciyar da sama da fursunoni 75,507 da ke gidajen yari 244 a kasar nan daga ranar 31 ga watan Disamban 2023 yayin da gwamnatin jihohi kuma ake tsammanin za su fara ciyar da masu laifin a jihohinsu kai tsaye.
Ministan kula da harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya shelanta hakan a jiya sa’ilin da ke kaddamar da shalkwatar hukumar kula da gidajen yari (NCoS) a Owerri da ke Jihar Imo.
- ‘Yansanda Sun Kama Mutumin Da Ya Kashe Matarsa A Adamawa
- Gawar Wani Tsoho Mai Shekara 115 Ta Yi Batan Dabo A Anambra
Aregbesola, ya ce, kashi 90 cikin 100 na fursunonin da ake da su, mutane ne da suka yi laifi wa jiharsu, don haka lokaci ya yi da jihohi za su fara zuba kudade su na ciyar da masu laifinsu.
Wannan bayanin na zuwa ne kasa da awa 24 da gwamnatin tarayya ta fito ta ce, tana kashe naira biliyan N22.4 wajen ciyar da fursunoni a fadin kasar nan, kuma har an shigar da hakan cikin kasafin kudin 2023.
Ya hakikance kan cewa matakin zai taimaka wajen rage cinkoson fursunoni a gidajen yarin kasar nan, Aregbesola ya na mai karawa da cewa kaso 80 na fursunoni su na zaman jiran shari’a ne.
Ya ce, akwai bukatar a sake waiwaye sosai kan tsarin shari’a a fadin kasar nan ta yadda za a ke yanke wa masu jiran shari’a hukunci a kan lokaci da daure wadanda suka dace.
A fadinsa, gwamnatin shugaba Buhari ta yi kokari sosai wajen gyara tsare-tsaren tafiyar da gidajen yari ta hanyar kara kudin da ake kashewa, kwaskwarima wa gidajen yari da kuma gina wasu sabbi dukka a kokarin rage yawan cunkoso.
Ministan ya kara da cewa, “Babban kalubalenmu shi ne yawan cinkoson fursunoni a gidajen yari, musamman a biranen da ke da yawan jama’a da yadda mu’amalar jama’a ke karuwa, don haka aikata laifuka zai karu a wannan wajen don haka ne sai ta kai an ajiye wasu a gidajen yari.
“Mun yi kokarin shawo kan wannan matsalar ta hanyar gina manyan gidajen yari guda shida a shiyyoyi shida da suke fadin kasar nan. Na Kano da na Abuja tunin aka kammala su, sauran ma za a kammala.”
Ya nanata cewa akwai gayar bukatar gyara kan tsarin shari’a ta yadda za a yi waiwaye ga dukkanin abubuwan da suke haifar da jinkirin shari’a domin a cewarsa kaso 70 zuwa ma 80 suna zaman jiran shari’a wanda hakan ba daidai ba ne, “Domin na tabbata a wasu lokutan ana tsare wadanda ma basu da laifi a yi ta ajiyesu a gidajen yari, ta hanyar gudanar da shari’a cikin hanzari ne za a gano mai laifi a yanke masa hukunci wanda bai da laifi a sake shi.”
“Wasu kuma koda sun yi laifin, hukuncin da za a yanke musu bai wuce watanni shida ba ya danganta da laifukan da suka aikata. To amma idan ba a yi shari’a ba sai mutum ya shafe tsawon lokaci a tsare.”
“Jihohi su tashi tsaye su gyara sashin shari’arsu su tabbatar ana yanke hukunci a kan lokaci da hanzarin yin shari’a. Wannan zai taimaka sosai wajen wanzar da adalci da kuma kawo karshen zare wanda ake zargi in ya yi laifi kuma a hukunta shi, in bai yi ba a sake shi,” ya shaida.