Wani sakamakon nazari ya nuna cewa, ana samun karuwar kwarin gwiwa tsakanin Sinawa masu sayar da kayayyaki dai-dai ko bayar da hidima kai tsaye, dangane da makomar kasuwanci, yayin da farfadowar tattalin arzikin kasar ke fadada.
Cibiyar bunkasa cinikayya ta kasar Sin (CGCC) ta ce alkaluman auna kuzarin masu sayar da kayayyaki kai tsaye, sun kai kaso 51.1 a watan Mayu, karuwar maki kaso 0.3 a kan na wata Afrilun, wanda kuma ke ta karuwa cikin watanni 5 a jere.
Makin da ya dara 50 na nuna samun ci gaba, yayin da kasa da 50 ke nuna koma baya.
A cewar cibiyar, yawan kudin da jama’a ke kashewa a bangaren yawon bude ido da na hidimar samar da abinci, shi ma ya karu yayin da ake ci gaba da samun farfadowar bangarorin a cikin gida, tana mai cewa, hutun ranar ma’aikata, ya kara kwarar mutane da kayayyaki.
Karuwar da alkaluman ke yi na nuni da farfadowar dukkan rukunonin bangaren sayar da kayayyaki, da kuma yakinin da su masu sayar da kayayyaki dai-dai suke da shi. (Fa’iza Musatapha)