ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Gurfanar Da Jami’an EFCC 2 Kan Zargin Kisan Abokin Aikinsu 

by CMG Hausa
3 years ago
EFCC

Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa (EFCC) ta ce, wani jami’inta mai suna Insifekta Abel Isah Dickson ya mutu bayan rashin jituwa da hatsaniya da ta shiga tsakaninsu da wasu abokan aikinsa guda biyu kan wasu kayayyakin da aka amso daga wajen wani da ake zargi a Jihar Sokoto. 

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce, kayayyakin sun hada da magunguna da wasu kudade.

ADVERTISEMENT
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bayar Da Lasisin Bude Jami’ar Koyo Daga Gida Da Karin Wasu 37

EFCC ta bayyana sunayen jami’an biyu sun hada da Mataimakin Sufuritendan hukumar EFCC, Apata Oluwaseun Odunayo da Insifekta na hukumar EFCC, Ogbuji Titu Tochukwu, wadanda tunin aka cafke su tare da gurfanar da su a kotu a jihar Sokoto kan zargin kisan kai.

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

Uwujaren ya kuma ce, shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, za su tabbatar an wanzar da adalci wajen hukunta jami’an, ya ce, an dakatar da jami’an biyu yayin da bincike ke cigaba da gudana.

Ya ce, Bawa ya sha alwashin ba zai lamunci wani dabi’a ta rashin da’a ba, “Shugabanmu, Abdulrasheed Bawa, ya kadu da wannan lamarin kuma ya jajantawa iyalan jami’in da ya rasa ransa.

“Ya kuma tabbatar da cewa jami’an da suka yi sanadiyyar rasa jami’in namu tabbas za su fuskanci hukunci har sai adalci ya wanzu.”

Kazalika, Bawa ya gargadi jami’ansa da su daina kokarin kauce wa ka’idar aiki da koyarwar da aka musu. Ya nuna cewa ba za su lamunci rashin bin matakan aiki da koyarwar da aka yi wa jami’an ba.

“A halin da ake ciki, an bisne jami’in namu da ya mutu a ranar Asabar 13 ga watan Mayun 2023 a Jos ta jihar Filato.”

“Matashin jami’in namu ya mutu ne a ranar 7 ga watan Mayun 2023 a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu DanFodiyo da ke Sokoto yayin da ke amsar kulawar Likitoci bayan raunukan da ya samu kwanaki biyu kafin nan a wani hatsaniyar da ya barke tsakaninsa da wasu jami’anmu biyu masu suna Apata Oluwaseun Odunayo da Insifekta Ogbuji Titu Tochukwu.

“Sun samu rashin jituwar ne kan wasu tsarin ajiye wasu kaya mallakin wani da ake zargi da ke tsare, hakan ya kai su ga yin fada, lamarin da hukumar nan ta yi tir da shi.

“Jami’an biyu an dakatar da su kuma an mikasu ga ‘yansandan Nijeriya inda suka gurfanar da su.

“An shigar da su kara ne kan zarge-zargen guda biyu da suka hada da hada baki wajen aikata kisan gilla a gaban babban Kotun Majistire, Gwiwa da ke Sokoto.”

“Laifukan biyun su na da hukunci a karkashin sashe na 60 da na 191 na dokar final kod ta Jihar Sokoto, 2019.

“Ba tare da nuna kyama ga binciken ‘yan sanda ba, za su kuma fuskanci karin matakan ladabtarwa bisa ka’idojin ma’aikatan hukumar.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani
Manyan Labarai

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Next Post
Darajar Hajojin Da Masana’antun Sin Ke Sarrafawa Ta Karu Zuwa Kaso 5.6 Bisa Dari A Afirilu

Darajar Hajojin Da Masana’antun Sin Ke Sarrafawa Ta Karu Zuwa Kaso 5.6 Bisa Dari A Afirilu

LABARAI MASU NASABA

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

Matasa Miliyan 80 Ne Ba Su Da Aikin Yi A Nijeriya

December 20, 2025
An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

An Nuna Jigo Da Tambarin Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Shekarar 2026 A Moscow

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.