Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na yau Laraba da aka saba yi duk mako a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Buhari ya dawo Nijeriya da maraicen ranar Talata bayan tafiyar da ya yi zuwa Landan don halartar bikin nadin Sarki Charles III.
- Mutum 1 Ya Mutu, Da Dama Sun Bace Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kwara
- An Tura Budurwar Da Ta Ci Zarafin Dan Sanda Gidan Yari
Zaman majalisar dai, shi ne na karshe da Buhari zai jagoranta, inda a mako mai zuwa ne, za a yi bankwana da gwamnatin Buhari.
A zaman na yau, majalisar ta yi duba a kan yarjejeniya kusan 60.
Zaman na yau, ya samu halartar sama da kashi 98 na ministoci da kuma kananan ministoci.
Bayan gaisuwa a tsakaninsu, sun ci gaba da gudanar da taron majalisar.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman majalisar akwai, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, mai bai wa shugaban kasa shawara a fannin tsaro Babagana Monguno.
Manyan ministocin da suka halarci zaman akwai, ministan kula da harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, ministan kimiyya da fasaha Olorunimbe Mamora; ministar kudi Zainab Ahmed; ministan sufuri Mu’azu Sambo; ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Ehanire; ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani Farfesa Isa Pantami, ministan wasanni, Sunday Dare, ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, ministan muhalli, Mohammed Abdullahi; ministan ayyuka Babatunde Fashola; ministan Abuja Mohammed Bello, ministan harkokin kasashen ketare, Geoffrey Onyeama; Atoni-Janar na tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami, ministar kula da harkokin mata Pauline Tallen; ministan ilimi Adamu Adamu, ministar jin kai da bayar da agajin gaggawa, Sadiya Farouk, ministan kula harkokin ‘yansanda, Maigari Dingyadi da kuma ministan yankin Neja Delta Umana Umana.
Kananan ministocin su ne, na masana’antu, kasuwanci da zuba jari Mariam Katagum; na harkokin kasar waje Zubairu Dada; kwadago da ayyukan yi Festus Keyamo, ilimi Goodluck Opiah, na muhalli Udi Odum.