Kamfanin LEADERSHIP ya kulla kawance da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), domin shirya “taro kan shaye-shayen miyagun kwayoyi, laifuka, da ci gaban kasa.”
An tabbatar da hakan ne a cikin wata takardar amincewa da hukumar ta NDLEA ta aike wa babban mataimakin shugaba/babban edita na Rukunan Kamfanonin LEADERSHIP Group Ltd, Azu Ishiekwene mai kwanan wata, 10 ga Mayu, 2023.
- Shugaban Tsimi Da Tanadi Ya Warware Mishkilar Dimbin Bashin Da Ake Bin Jihar Kaduna
- Xi Da Mai Dakinsa Sun Jagoranci Bikin Maraba Da Baki Mahalarta Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Wani bangare na wasikar mai dauke da sa hannun Daraktan Yada Labarai da Hadin Gwiwa na NDLEA, Femi Babafemi ya bayyana cewa “Na rubuto ne domin na isar da amincewar shugaba kuma babban jami’in zartarwa game da shawarar da kuka gabatar ta “Shirya Babban Taro Kan Yaki da Shaye-Shayen Miyagun Kwayoyi, Laifuka, Da Ci Gaban Kasa.”
“Muna godiya da kokarin da kuke yi na ganin al’ummarmu ta barranta da ta’ammali da muggan kwayoyi, kuma ku lura cewa yaki da shaye-shayen miyagun kwayoyi abu ne mai matukar wahala kuma yana bukatar hadin gwiwa daga dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da kafofin yada labarai.
“Hukumar tana aiki tukuru don ganin an rage yawan abubuwan da suka shafi shaye-shayen da fataucin muggan kwayoyi a cikin kasar nan, don haka suna maraba da gudummawar da ‘yan Nijeriya masu kishin kasa da kungiyoyi, da kamfanoni irin ku ke bayarwa don cimma wannan buri.
“Yayin da muke tabbatar muku da shirye-shiryenmu na yin hadin gwiwa tare da ku don samun nasarar taron, muna kara yi muku fatan alheri da kuma fatan shirya abubuwan da za su yi matukar tasiri a taron.”
Idan dai za a iya tunawa, a bisa fargabar yadda matasa ke kara tsunduma harkar shaye-shayen miyagun kwayoyi a fadin kasar nan, Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP ya yi kiran a hada hannu da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa domin samar da ingantacciyar hanyar yekuwa a kafafen yada labarai game da yadda za a shawo kan matsalar.