A yau Litinin 22 ga watan Mayu ne ake sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da matatar man Dangote da za ta tace ganga 650,000 a kullum.
A cewar wata sanarwa da kamfanin Dangote ya fitar a shafinsa na Twitter, matatar man za ta fitar da Man fetur (PMS) da diesel (AGO) da man jiragen sama da kuma kananzir (DPK) da sauran kayayyakin da ake tace wa.
Da yake magana game da katafariyar masana’antar, babban jami’in matatar man Dangote, Sanjay Gupta, ya bayyana cewa “Duk abin da ke cikin wannan masana’anta mai girma, shi ne irinshi na farko a duniya. Ita ce matata mai rumbu daya tilo babba a duniya.
“Babu wani rumbun mai daya tilo wanda zai iya tace ganga 650,000 a kowace rana a ko’ina a duniya sai wannan,” inji Gupta
Ana sa ran za a kaddamar da matatar ne a jihar Legas.