A jiya ne aka rufe taron kolin kungiyar G7 na tsawon yini uku a birnin Hiroshima na kasar Japan. Sai dai hadaddiyar sanarwar da taron ya fitar ta kara wa batutuwan da suka shafi kasar Sin gishiri, inda mahalarta taron suka yi barazanar daukar matakai na tinkarar abin da suka kira wai “matsin tattalin arziki”, matakin da ya bayyana yadda kasashen yammacin duniya da ke karkashin jagorancin kasar Amurka suke yin amfani da kungiyar G7 wajen yin babakere da ma neman dakile kasar Sin.
A zahiri dai, Amurka ce kasar da ke yin matsin tattalin arziki, duba da yadda ta sha daukar matakai na sanya takunkumi da kayyade fitar ko shigar da kayayyaki da kara sanya harajin kwastan da sauransu, don yi wa sauran kasashe matsin tattalin arziki, baya ga kuma yadda take tilasta yin amfani da dokokinta na cikin gida a kan sauran kasashe, da ma tilasta wasu kasashe katse huldar tattalin arziki da su. Hakika matakan da ta dauka na matsin tattalin arziki ba sa lisaftuwa, wadanda suka lalata tsarin samar da kayayyaki na duniya tare da jawo baraka ga kasuwar duniya.
Ko da kawayenta da ke cikin kungiyar G7 ma ba su tsira daga matakanta na matsin tattalin arziki ba. In mun duba tarihi, kamfanin Toshiba na Japan da Siemens na Jamus da kuma Alstom na Faransa, wadanda dukkaninsu kamfanoni ne na kasashe kawayen kasar Amurka, duk sun fuskanci irin matakan da Amurka ta dauka, sakamakon yadda suka zama kalubale gare ta. Saboda a ganin kasar Amurka, moriya ce kawai za ta dore a maimakon zumunta.
Sai dai abin takaici ne yadda su kasashe mambobi kungiyar G7 da Amurka ta yi musu illa, har yanzu suke hada kai da Amurka din suke yi wa wasu illar da suka taba fuskanta.
‘Yan siyasa da kafofin yada labarai na Amurka sun kware wajen jirkita gaskiya bisa tasirinsu na iya magana, kuma zancen nan na wai “matsin tattalin arziki” mataki ne da Amurka ta dauka don takura wa kasar Sin. Sanin kowa ne kasar Sin na nacewa ga bin hanyar samun ci gaba cikin lumana, wadda kuma take tsayawa tsayin daka a kan manufar bude kofa ga juna don cin moriyar juna. A cikin shekaru 10 da suka wuce, gudummawar da ta samar wa bunkasuwar tattalin arzikin duniya ta zarce wadda kasashen G7 suka bayar baki daya.
Hasashen da bankin duniya ya yi ya kuma shaida cewa, ya zuwa shekarar 2030, shawarar “ziri daya da hanya daya” da kasar Sin ta gabatar za ta fitar da mutanen duniya miliyan 7.6 daga matsanancin talauci. Baya ga haka, manyan ababen more rayuwa da kasar Sin ke ginawa a sassan duniya na taimakawa kasashe daban daban raya tattalin arzikinsu. Da hakan muke iya gano cewa,kasar Sin tana samar da zarafi da ci gaba ga duniya a maimakon kalubale da barazana.
Kasancewarsu kasashe masu sukuni, ya kamata kasashen G7 su kara mai da hankali a kan yadda za su taimaka ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ma bunkasuwa a duniya, a maimakon neman lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin duniya da ma dalike ci gaban sauran kasashe.(Lubabatu)