A ranar Talata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka guda bakwai da ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya ta kammala a fadin kasar nan.
Mista Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, wanda ya tabbatar da wannan ci gaban a wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, ya ce ayyukan sun yi daidai da kudurin gwamnatin Buhari na inganta da fadada kayayyakin more rayuwa.
- Majalisar Lafiya Ta Duniya Ta Sake Yin Watsi Da Shawarar Dake Shafar Taiwan
- Shugabancin Majalisa Ta 10: Katsalandan Din Gwamnati Ya Janyo Turka-Turka – Hon. Bello
Ayyukan a cewar Adesina, sun kunshi manyan gadaje uku, sakatariyar gwamnatin tarayya guda uku da kuma hanya daya, yana mai cewa taron mai dimbin tarihi zai gudana ne a kan gadar Neja ta Biyu da aka fara a 2005.
Ya kara da cewa, a shekarar 2014, an yi yunkurin fara aikin ta hanyar hadin gwiwar kamfanoni masu zaman kansu (PPP) amma hakan bai yi nasara ba.
Sai dai ya bayyana cewa an fara aikin ne a shekarar 2016 da asusun bunkasa ababen more rayuwa na shugaban kasa (PIDF).
Mai taimaka wa shugaban kasar ya bayyana cewa sauran ayyukan da shugaban zai kaddamar sun hada da; gadar Loko-Oweto wadda ta ratsa kogin Benuwai domin hada Benuwai da Nasarawa da gadar Ikom da ke Kuros Riba.
“Aikin titin shi ne da aka kammala sashen sama da kilomita 200 na babbar hanyar Kano zuwa Kaduna da kuma sabbin sakatarorin gwamnatin tarayya guda uku.
“Babban Sakatarorin Gwamnatin Tarayya da ke Awka na nan, a karamar Hukumar Awka ta Kudu, a Anambra kuma yana kan fili mai fadin Hekta 5.106.”
Ya bayyana cewa an fara bayar da aikin ne a ranar 9 ga watan Disamba, 2011 amma a zahiri an kammala shi kuma ma’aikatar ayyuka da gidaje ta karbe shi a ranar 14 ga watan Yuli, 2022.
Sakatariyar tana da jimillar ofishi 498, zauren taro, dakunan kwamitoci guda hudu, ofishin gidan waya da sauransu.
Bugu da kari, Sakatariyar ta na da wuraren ajiye motoci da magudanan ruwa, kantin ma’aikata, injin kashe gobara da sauran muhimman wurare.
Na biyu, sakatariyar Gusau da ke Unguwan Dan Lawan a Jihar Zamfara.
Aikin yana kan fili mai fadin hekta 7.5 kuma ma’aikatar ta kammala shi a kusan 30 ga watan Nuwamba, 2022.
A cewar Adesina, na uku da za a kaddamar shi ne sakatariyar gwamnatin tarayya Yenagoa, wadda ke kan titin Alamieyeseigha, a Bayelsa.
“Yana kan fili mai fadin hekta 7.5 kuma an bayar da shi ne a ranar 9 ga watan Disamba 2011 amma kusan an kammala shi kuma ma’aikatar ta karbe shi a ranar 30 ga watan Nuwamba, 2022.”
Idan dai za a iya tunawa, shugaba Buhari ya kaddamar da na hudu, wato Sakatariyar gwamnatin tarayya da ke garin Bukar Sidi da ke kan titin Jos, Lafia, Nasarawa a watan Fabrairun wannan shekara.