Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta kasa (NHRC) tare da hadin guiwar kungiyar farar hula ta Kano (KCSF) sun kaddamar da wani kwamiti da zai binciki zargin kashe mutane uku da aka yi a yayin zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar APC a jihar Kano.
Dan takarar gwamna a jam’iyyar, Sha’aban Sharada, ya yi zargin cewa an kashe wasu magoya bayansa yayin da wasu suka jikkata a zaben da aka gudanar a ranar Alhamis din da ta gabata.
- 2023: Kakakin Majalisar Kano, Chidari Ya Lashe Tikitin Takarar Majalisar Wakilai Na APC
- Wata Yarinya ‘Yar Shekaru 4 Ta Mutu Bayan Ta Faɗa Rijiya A Kano
Kwamitin mai mutum 11 zai kasance tare da kodinetan NHRC, Shehu Abdullahi, da shugaban KCSF, Ibrahim Waiya.
Waiya, ya ce ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa nan da makwanni uku domin gaggauta gudanar da bincike kan zargin.
A halin da ake ciki kuma, wata gamayyar kungiyoyin farar hula a jihar ta yi kira da a soke zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a jihar bisa wasu kura-kurai da suka yi da yin magudin zabe.
Kungiyar ta yi zargin cin zarafin da jami’an gwamnati suka yi da kuma hana wakilan Sharada kada kuri’a a zaben.
Idan dai za a iya tunawa, an bayyana mataimakin gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin.