Reshen Dalibai na Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula na Arewa, da ke Jihar Kano (CNG-SW), sun yi barazanar rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin kasa da kuma manyan titunan Arewa in har gwamnatin tarayya da ASUU ba su kawo karshen takaddamar yajin aikin da ke tsakaninsu ba.
Daliban sun yi barazanar rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 da ke Arewacin Nijeriya.
- Bayan Ruwan Wuta: Masu Garkuwa Sun kama Basarake A Jos
- Hajjin Bana: Saudiya Ta Hana Amfani Da Gas Din Girki A Lokacin Aikin Hajji
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da ko’odinetan kungiyar Ambasada Khaleefa Nura Babujee, ya fitar ga manema labarai a Kano.
Ko’odinetan kungiyar, Babujee, Ya ce CNG-SW ta shiga damuwa kan yadda yajin aikin ASUU yaki ci yaki cinyewa.
A cewar ungiyar yajin aikin ya jefa ‘ya’yan talakawa cikin mawuyacin hali.
Ya kara da cewa tuni kungiyar ta yi shirin daukar gabaran rubuta korafi ga sarakunan gargajiya, malaman addini, jami’an gwamnati da jami’an tsaro a kan su saka baki a kawo karshen yakin aikin.
“Idan haka ba ta samu ba, to za mu rufe filayen jirgin sama da tashoshin jirgin kasa tare damanyan titunan Arewacin Nijeriya.
“Za kuma mu rufe ofisoshin jam’iyyun siyasa a jihohi 19 na yankin Arewa,” in ji CNG-SW
Ya zuwa yanzu ASUU da gwamnatin tarayya sun gaza cimma matsaya don kawo karshen yajin aikin da suka jima suna yi.
A baya-bayan nan ma sai da dalibai a wasu jihohin Nijeriya da suka hada da Kano, Legas, Kaduna, Anambra da sauransu suka gudanar da zanga-zangar adawa da yajin aikin na ASUU.
Har ila yau, masu ruwa da tsaki a fannin ilimi sun sha kira ga bangarorin biyu da su yi kokarin samun fahimta don dalibai su koma bakin karatunsu.