Abokai, kwanan baya, ministar kudin kasar Amurka Janet L. Yellen, ta yi gargadi kan matsalar kasa biyan basusuka da kasar za ta fuskanta. Abin da zai kawo illa ga tattalin arziki da hada-hadar kudin duniya.
Dalilin da ya haifar da irin wannan rikici shi ne, gwamnatin Amurka ta kashe kudi babu iyaka kamar yadda take so, saboda matsayin kudin dalar Amurka dake na farko a duniya, yana mallakar kasuwar kudaden kasa da kasa.
Masana na nuna cewa, gwamnatin Amurka ta dade tana samar da kudaden dalar masu dimbin yawa, bisa matsayinsa na kudin da aka adana, abin da ya ingiza gwamnatin da ta kara sayar da basusuanta ga ketare.
Ya zuwa yanzu, rabin saye da sayarwa da ake yi a duniya bisa kudin dalar Amurka ne, hakan ya sa Amurka ke iya amfani da kudinta don biyan basusukan da ake binta. Ban da wannan kuma, Amurka tana satar ci gaban bunkasuwar tattalin arzikin sauran kasashe, ta amfani da matsayin babakere da take da shi a fannin kammala cinikayya da manyan ababen hada hadar kudade, ta hanyar sayar da dimbin basusuka ga ketare. Idan rikice-rikice sun barke, sai ta bar sauran kasashe su yi asara.
Ya kamata, mu fidda wata hanyar ciniki ta kasa da kasa, da za ta dace bisa adalci, don yaki da babakeren dalar Amurka a duniya, don kawar da rikice-rikice dake fadawa kasashen duniya.
(Mai zana da rubuta: MINA)