Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kai hari a inda ake hakar ma’adanai a yankin ‘Yar-Nasarawa a cikin karamar hukumar Maru da ke jihar Zamfara.
A lokacin harin, ‘yan bindigar sun kuma hallaka mutane 29 da sace Babura 152.
Wajen hakar ma’adanan, tana daura da yankunan Malele, Ruwan Tofa da kuma ‘Yansawayu da ke kan hanyar masarautar Dansadau.
An ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kai a harin ne akan baburansu da adadi masu yawa a yayin da ma’aikata sama da 300 ke kan hakar ma’adanai a lokacin.
Rahotanni sun ce, duk da haramta hakar ma’adanai a jihar, wasu mutane sun cigaba da hakar ta haramtacciyar hanya a wasu sassan jihar.
A cewar majiyoyin, tawagar ‘yan ta’adda biyu ne suka kai harin na hadin guiwa da Lawali Damina da Ali Kachalla ke jagoranta.
Wani mazaunin a yankin Ruwan Tofa wanda ya tsallake Rijiya da baya, ya bayyana cewa, wadanda suka rasa rayukansu a lokacin harin, an yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.
A cewarsa, gungun ‘yan bindigar sun kai hari ne da kimanin karfe 4 na yamma, a yayin da masu hakar ma’adanai sama da 300 ke wurin a lokacin.
Ya ce, ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da babura 152.
A cewarsa, amma a yanzu al’amura sun daiddai duk da cewa, babu jami’in tsaro ko daya da yazo yankunan.
Amma da aka tuntubi gwamnati da kuma rundunar ‘yansandan jihar kan harin, rundunar ta ce, ba a kawo mata wani rahoto kan wannan harin ba.
Sai dai, an ruwaito kwamishinan kula da harkokin tsaro da kula da harkokin cikin gida na jihar, MamanTsafe ya ce, yana sane da wajen hakar ma’adanan da ake magana akai, amma bai da wata masaniya kan harin, amma zai bincika.