Sabuwar matatar man dangote da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a farkon makon nan za ta kasance mai matukar alfanu ba ma kawai ga Nijeriya ba har da yankin Afirka baki daya. Kadan daga ciki shi ne yadda matatar za ta taimaka wa Nijeriya ceto dalar Amurka biliyan 30 da take kashewa wajen tace mai daga kasashen waje, tare da habaka shigo da kudaden kasashen waje akalla Dala biliyan 10.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sauran shugabannin Afirka biyar suka ba da tabbacin Afirka za ta samu sa’ida wajen zuwa kasashen turawa sayo tataccen mai da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci. Shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce matatar za ta taimaka wajen ciyar da Nijeriya gaba ta fuskar dogaro da kai da samar da abinci, da dai sauran muradun kasa.
Da yake jawabi a wurin kaddamar da rukunin matatar man ta Dangote da ke Legas a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, 2023, gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa matatar Dangote da ke da karfin sarrafa gangar danyen mai 650,000 a kowace rana ita ce matatar mai mafi girma a duniya kuma za ta kara habaka samun kudaden waje wanda zai kara karfafa asusun ajiyar gwamnati da kuma daidaita farashin kudaden musaya.
Ya lura cewa, ana sa ran tasirin ajiyar zai fito fili baro-baro a cikin asusun ajiyar Nijeriya na waje ta hanyar rage matsin lamba kan ma’aunin biyan kudi, yana mai cewa “har ila yau akwai fa’idodi masu yawa da za mu samu daga fitar da kayan da matatar za ta rika sarrafawa tana fitawar zuwa sauran duniya.
“Bugu da kari matatar man za ta taimaka wa Nijeriya wajen tsumin dalar Amurka biliyan 30 da ake kashewa wajen shigo da man fetur, sannan ana hasashen tattalin arzikin kasar zai amfana da karin dalar Amurka biliyan 10 na kudaden musaya a duk shekara ta hanyar fitar da tataccen man fetur zuwa kasashen waje, wanda hakan zai kara habaka asusun ajiyarmu a hukumance da saukaka wahlhalun da ake sha na musayar musayar kudi.
“Wannan aikin zai kuma ba da tallafi ga ayyukan kasafin kudi na gwamnati kamar yadda zai taimaka wajen saukaka matsalolin makudan kudin da ake warewa a kan tallafin man fetur da kuma samar da tanadin kasafin kudi mai inganci. Bayanai da ake samu sun nuna cewa, a cikin shekaru biyar, tallafin man fetur a Nijeriya ya haura sama da ninki tara daga kimanin Naira biliyan 154 a shekarar 2017 zuwa sama da Naira Tiriliyan 1.43, kafin ya kuma tashi zuwa Naira Tiriliyan 4.4 a karshen shekarar 2022.
“Hasashen na nuna cewa wannan adadi zai iya zarce Naira tiriliyan 7 a cikin shekaru uku masu zuwa idan ba mu magance shi yadda ya kamata ba. Alhamdu lillahi, matatar mai ta Dangote za ta iya ceto wa Nijeriya kimanin Naira Tiriliyan 5 zuwa Naira Tiriliyan 7 a duk shekara a cikin kasafin kudin Gwamnatin Tarayya nan da shekaru biyar masu zuwa,” in ji shi.
A halin da ake ciki, Emefiele ya bayyana cewa, rukunin Dangote ya fara biyan wasu lamunin kasuwanci tun kafin kaddamar da wannan cibiyar wanda ya ce yana nuna iya kasuwancin kamfanin da shugabansa. Bayan biyan wani kaso mai yawa, basusuka sun ragu sosai daga sama da dala biliyan 9 zuwa dala biliyan 3.
“A daidai wannan lokaci dole ne in yaba wa dukkan bankunan Nijeriya da ke cikin gida, wadanda ba wai kawai sun hada hannu da aikin ta hanyar samar da kudade masu inganci ba, amma suna da masaniya kan muhimmancin aikin ga al’ummarmu. Sun ba da tallafi mai yawa da fahimta ta musamman, hatta lokacin biyan kudin ruwa da adadin abin da za a rika biya sun ragu sosai,” in ji shi.
A nasa jawabin, shugaba Buhari, ya ce matatar man Dangote ta kara nuna jajircewar Alhaji Aliko Dangote, inda ya kara da cewa kamfanin zai ciyar da Nijeriya gaba wajen dogaro da kai wajen samar da abinci, da dai sauran muradun kasa.
A cewarsa, matatar mai ta Dangote da ke zama matatar mai mafi girma a Nahiyar Afirka, tare da masana’antar takin zamani, za ta taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen aikin noma a matsayin sana’a ta ainihi da ake cin gajiyarta koyaushe da kuma bayar da gudunmawa wajen daidaita harkar man fetur a kasar.