Rubutun namu ba zai takaita ba ne ga iyaka wadancan jihohi 17 da ake ta wassafa basukansu na gida da daji, tun farkon wannan dogon tsokaci. La-budda, wajibinmu ne mu sake nitsawa cikin taza da tsifa zuwa ga wasu jihohin na daban da ke cikin wannan taraiyar Kasa tamu ta Najeriya.
Bayan gabatar da karin wasu bayanai na kamar makonni biyu masu zuwa, abinda za mu ja akalar wannan dogon sharhi namu zuwa gare shi shi ne, shin, mene ne mafita game da irin wadannan dama-tsirin basuka da shugabanni a wannan Kasa ke ci dare da rana ba tare da yin wata nadama ba?
Ko da yake, cikin sabbin jihohi takwas (8) din da yanzu za mu gabatar da nasu sabgar bashin, akwai guda daga cikinsu, Ebonyi, wadda a baya kadan mun gabatar da wani abu nata game da lamarin bashin.
Kasantuwar yanzu za a gabatar da wani rahoto ne da ke dauke da daukacin jihohin takwas (8) waje guda, hakan na nuna wajibcin kawo su tamkar irin yadda rahoton ya gabatar da su jumla, rashin yin hakan, zai samar da yanayin gibi ne a labarin. Ga jumlar jihohin 8 din kamar haka; jihar Bayelsa, jihar Gombe, jihar Kebbi, jihar Taraba, Jigawa, jihar Yobe, jihar Zamfara, sai kuma jihar Ebonyi.
Hukumar Kididdiga ta Kasa, “National Bureau of Statistics (NBS)”, cikin wani rahoto da ta fitar a ranar 24 ga Watan Afurilun wannan Shekara ta 2023, ta fadi cewa, wadancan jihohi 8 da aka ambata a sama, kusan Shekaru hudu (4) da suka gabata zuwa yau (2023), sun gaza jan-hankalin masu zuba jari daga ketare zuwa jihohin nasu.
Bugu da kari, daga ofishin hukumar da ke kula da sabgogin basukan a Kasa, “Debt Management Office (DMO)” an samar da wani rahoton da ke nuni da cewa, cikin Shekarar 2019, idan aka hada wadancan jihohi takwas jumla, za a iske a na binsu zunzurutun bashi har kimanin naira miliyan dubu dari bakwai da goma da digo uku (N 710.38bn) ne.
Cikin Shekarar 2022 kuwa, sai ga bashin da ake bin wadancan jihohi 8 ya tashi daga naira biliyan 710.38 zuwa naira biliyan dari tara da hudu da digo hudu (N 904.47bn) cifcif. Wato ke nan, an sami karin naira biliyan dari da casa’in da hudu (N 194.09bn) cikin Shekaru biyu kacal da suka karu.
Har ila yau, a wata kididdigar, an fadi cewa, cikin Shekarar 2019, an tabbatar da a na bin wadancan jihohi takwas zunzurutun bashin gida har kimanin naira miliyan dubu dari biyar da sittin da hudu da digo shida (N 564.69bn). Sannan kuma a bashin ketare, a na bin jihohin dalar Amurka kimanin miliyan dari uku da sha-bakwai da digo biyu ($ 317.21m).
An tabbatar da cewa, uku daga cikin wadancan jihohi 8 ne a kan gaba wajen cin bashin gida sama da sauran jihohin biyar a cikin Shekarar 2019. Jihar farko ita ce Bayelsa, wadda ta kandami bashin biliyoyin nairori har kimanin biliyan dari da arba’in da bakwai da digo tara (N 147.93bn). Jihar da take biye da ita, ita ce jihar Gombe, wadda ake binta tsabar kudi har kimanin naira biliyan tamanin da hudu (N 84.01bn). Jihar Taraba ce ta uku, wadda ake binta bashin gida har wajen naira biliyan tamanin da biyu da digo uku (N 82.32bn).
Cikin Shekarar 2022 kuwa, jihohin Bayelsa da Gombe na nan a matsayin na daya da na biyu a batun bashin biliyoyin kudaden gida da suka ci. Inda Bayelsa ke da naira biliyan 146.37 a kanta. Jihar Gombe ce ke biye da ita da zunzurutun kudade har naira biliyan 139.32. Sai dai a wannan lokaci ba jihar Taraba ce ta uku ba kamar yadda ya afku a Shekarar 2019 da ta gabata, don kuwa jihar Zamfara ce ta kere ta da wuri na gugar wuri har kimanin naira biliyan 122.2, sai Taraban da zamto ta hudu, da naira biliyan 87.96.
Idan aka koma ga batun bashin ketare cikin Shekarar 2019 kuwa, sai a ga cewa jihohi irinsu Ebonyi da Bayelsa da Kebbi ne na daya da na biyu da na uku cikin jerin jihohin, wadanda suka naushe kowa wajen makare cikunansu da basukan. Dala miliyan 65 da digo biyu ($ 65.2m) ne jihar Ebonyi ta ranto. Ita kuwa jihar Bayelsa a matsayin ta biyu, ta yi habzi ne dalar Amurka miliyan hamsin da tara da digo biyar ($ 59.55m). Jihar Kebbi ce ta uku, mai adadin kudi dalar Amurka miliyan arba’in da hudu ($ 44.03m).
Cikin Shekarar 2022 game da kididdigar bashin ketare, sai aka wayigari lissafi na canjawa. Domin kuwa ya faru cewa, jihar Bayelsa ta kere jihar Ebonyi, tare da zama ta daya, da adadin kudade har kimanin dalar Amurka miliyan sittin da digo uku ($ 60.39m). Jihar Ebonyi ce ta biyu, da dalar Amurka miliyan hamsin da takwas da digo biyar ($ 58.57m). Jihar Taraba ce ta uku a wannan jikon, tare da shan gaban jihar Kebbi, tana da dalar Amurka miliyan arba’in da shida da digo hudu ($ 46.47m) ne. Jiha ta hudu wato Kebbi, tana da zunzurutun kudi ne har kimanin dalar Amurka miliyan arba’in da digo tara ($ 40.93m).
Abin haushin da ban takaicin shi ne, gashi an fada cewa daukacin jihohin 8, sun kasa jawo hankalin mutanen ketare, na, su zuba jari a cikin jihohin nasu, kuma gashi babu wasu aiyuka da suka gabatar cikin jihohin nasu, wadanda za su rika haihuwa, suna tara musu kudaden shigar da za su yi amfani da su ta fuskoki biyu. Fuska ta farko, da irin wadannan kudaden shigar ne za su fara daura azamar biyan irin wadancan lallaftun basukan da tuni sun bisne jama’ar jihohinsu da su. Bashin da hatta baban wanda za su ci gaba da biyan kudaden nan gaba ma ba a haifa ba. Eh mana, wani bashin jihar ma, sai an wuce shekaru 20, wasu 30, wasu 40, wasu 50 wasu sama da Shekaru hamsin din za a wuce a na biyansa. Fuska ta biyu, da a ce irin wadancan gwamnoni na karshen zamani sun yi amfani, ko sun sanya zunzurutun kudaden basukan ta hanyoyin da suka dace, to da, ba ya ga samun sukunin biyan basukan, a lokaci guda kuma har ma za su sami damar gabatarwa da al’umominsu manyan aiyukan ci gaba da sashin kudaden.
Babu shakka, duba da irin wannan yanayi na saki na dafe da shugabanni suka tsunduma wannan Kasa ciki, ta fuskar ta’adar rungumar basukan gida da na daji, abin Allah wadai ne ga duk wani mai kishin kasa. Lokaci ya yi da daidaikun mutane da kungiyoyi, na su tashi su kalubalanci wannan ta’adar tun gabanin riskar kai a yanayi na mutuwar kasko, koko a ce yanayi na Da kwance Uwa kwance!
A can baya mun gabatar da kalubalantar da Kungiyar AESID ke yi wa gwamna Dabid Umahi, game da yunkurinsa na nutsar da jihar ta Ebonyi cikin tekun bashi. Har ila yau, akwai wasu korafe-korafe masu ma’ana da suke gabatarwa abin la’akari, cikin yin hannun rigarsu da gwamnatin Umahi. Ga korafe-korafen kamar haka;
i- Sun ma zargin gwamnan da ta’adar ciwo bashin da a wani lokaci ma ba ya bin ka’idar da doka ta shimfida idan a na son amsar bashin. Hatta ma wani bashin za a ga bai damu da tuntubar ‘yan majalisar dokoki ta jihar ta Ebonyi ba.
ii- Bugu da kari, sun zargin Umahi da cewa, duk da zunzurutun biliyoyin kudade da yake ciwowa jihar bashi akai akai, amma ya kasa samarwa da jihar ta Ebonyi ko da kuwa wata masa’anta ce da za a dinga sayar da ko ruwan sha ne a leda a na saidawa jama’a, don kara bunkasar tattalin arzikin jiha.
iii- Sun zargi gwamnatin da yin almubazzaranci da kudaden al’umar jihar, a yunkurinsa na son kashe zunzurutun kudade masu rai har kimanin naira miliyan dari shida (N 600m), kawai don shirya bikin taya murna ga gwamnatinsa da ta yi Shekaru bakwai (7) cifcif bisa karagar mulkin jihar.
Irin wadancan zarge zarge da Kungiyar AESID ke wa gwamna Dabid, kusan duk wata jiha da ka je a Najeriyar yau, za ka yi karo da irinsu, tun da halaiyar gwamnonin idan an zo ga batun karbar bashin gida ko na ketare, duka sai a ga ai dodo guda ne suke yi wa tsafi!. Cikin rubutunmu na baya, an ta gabatar da korafin cewa, gwamnonin, ba su damu da sanya kudaden da suke rantowa cikin aiyukan da za su haife tare da samun damar biyawa kansu bashi ba, shi ma gwamna Umahi bai zamto waren gwanki ba, don kuwa, ya lallaba zuwa ga wani Bankin Musulunci inda ya aro kudi kimanin dalar Amurka miliyan dari da hamsin ($ 150m) don gina hanya kawai a jihar.