Ranar Alhamis 18 ga watan Mayu 2023 za ta kasance ranar da zan dade ban manta ba da gaggawa, don a ranar ce Allah ya yi wa abokina kuma abokin aikina, Malam Sabo Ahmad Kafin-maiyaki rasuwa bayan ya yi fama da jinyar kwana 29 sakamakon faduwa da ya yi sanadiyar cutar hawan jini.
Malam Sabo wanda ainihin sunansa na yanka shi ne Isma’il amma, kasancewar an haife shi ne a lokacin da iyayensa ke tsananin saukin samun haihuwa sai aka rika kiransa da Sabo ta haka ne sunan ya danne anihin sunansa na yanka, (su biyu ne kacal iyayensu suka haifa, sunan yayansa Garba wanda aka fi sani da Datti) an haife shi ne a garin Kafin-maiyaki da aka fi sani Kwanan Dangora da ke karamar hukumar Kiru ta Jihar Kano, amma iyayensu sun taso daga wani kauyen garin Karaye.
Bayan tasowarsa ya shiga harkar kasuwanci kamar yadda mahaifinsa yake yi na safarar kayayyaki zuwa Kudancin kasar nan, daga baya ya shiga makarantar firamare a nan Kwanan Dangora, ya kuma yi sakandarensa a GSS Kafin-Maiyaki inda daga nan ya wuce jami’ar Ahmadu Bello Zariya ya yi digiri a fannin harshen Hausa, bayan kammala karatunsa ne sai Sabo ya tsunduma harkokin rayuwa inda ya shiga kasuwanci da aikin jarida a matsayin dan jarida mai zaman kansa a wannan bangaren sanannun gidajen jaridun da ya yi aiki da su sun hada da Almizan, Sadarwa, Mahanga da Taskira daga nan kuma ya kafa jaridarsa ta kansa mai suna Alzajeera. Aljazeera ta samu karbuwa sosai amma saboda yanayi irin na Nijeriya wanda masu kokarin tsayuwa da kafafuwansu basa samun dama, a dole yana gani jaridar ta durkushe ta shiga kundin tarihi kamar yadda sauran jaridun Hausa suke shiga a Nijeriya.
A na cikin wannan halin ne Sabo Ahmad ya kama aiki a a kamfanin Leadership, a lokacin ana buga jaridar Leadership A Yau a matsayin mai tantance rubutu ‘Prtoofreader”, bai dade a mukamin ba ya zama mataimakin Edita na bangaren jaridar da ke fitowa daga Litinin zuwa Alhamis (Daily), a nan ma bai dade ba inda ya za ma Editan jaridar mai fitowa Asabar (Leadership A Yau Asabar) ya kuma rike mukamin har zuwa lokacin da aka sake mayar da shi Editan Lahadi (LEADERSHIP A Yau Lahadi), kafin daga bisani bayan an sauya wat sarin sashen Hausa na LEADERSHIP fasali, ta koma fitowa mako-mako a matsayin LEADERSHIP Hausa, ya koma kula da bangaren fassara da tantance rubutu na sashin.
Malam Sabo mutum ne da za ka iya fassara shi ta hanyoyi daban-daban don da farko yana da tsantsenin lallabawa da mutane, ba ya son ya ga ya saba wa abokan huldarsa, ta haka wasu ke ganinsa a matsayin wanda ba ya son kulawa da mutane, don za ka iya zama da Malam Sabo na tsawon lokaci amma ka kasa sanin halin da yake ciki, mutumm ne mai zurfin ciki. Yana iya kwana bai ci abinci ba, amma saboda halinsa na kin bayyana halin da yake ciki wanda ke kusa da shi ba lallai ya fahimci haka ba. Haka kuma yana da kokarin boye halin rashi a duk lokacin da ya tsinci kansa a ciki.
A daidai wannan lokacin kuma shi mutum ne mai yawan kyauta, don kuwa Malam Sabo na iya bayar da kudinsa na karshe da ke a aljihunsa ga wanda yake ganin ya fi shi bukata shi kuma ya zauna ba ko kwabo, duk wani da ke zaune kusa da shi zai iya tabbatar maka da wannan dabi’a tashi.
Masu iya magana na cewa, ciwon ajali ba ya jin magani, na kara samun yakini da wannan maganar ne a kan ciwon ajalin da ya samu Sabo. Abin ya faru a ranar Laraba 19 ga watan Afrilu, bayan mun kammala aikin Jaridar makon, tare da shi muka yi aikin bibiyar shafukan jaridar kamar yadda aka saba, muna gyare-gyare na karshen, da yake ana gab da buda baki sai muka ba Sabo sakon abubuwan da za mu ci na buda baki (rashin girman kai na daga cikin halayensa) suka tafi da Malam Idris Aliyu Daudawa zuwa unguwar Utako. Muna cikin jiran a kawo mana abin buda baki ne sai ga wayar Idris Daudawa inda yake sanar da cewa Malam Sabo ya fadi, faduwa irin ta masu cutar hawan jini, daga nan ne muka kai shi wani asibiti a nan unguwar Utako a inda suka yi kokarin su a kanshi har zuwa washe garin Alhamis, dama a ranar muke komawa gida kuma washe gari ne za a gudanar da bubukuwan sallah, haka aka dora shi a mota muka kamo hanyar Zariya, tun da ya fadi ba ya iya amfani da wasu sassan jikinsa, kamar kafafuwa, hannaye ba ya kuma iya magana.
Kai-tsaye muka wuce da shi asbitin Sabannah Polyclinic da ke Hayin Dogo Samaru Zariya inda ya yi kwanaki 23. Da farko jikin ya fara sauki don har yana amsa gaisuwa yana kuma furta wasu kalmomi in yana bukatar wani abu, yana kuma iya rike biro yana kokarin rubuta wasu kalmomi, ko a lokacin da abokan karatunsa na GSS Kafin-Maiyaki suka kai masa ziyara a asibitin, ya rubuta sunayen dukkansu, abin da ya kara karfafa mana gwiwa a kan samun saukinsa, amma kuma daga baya sai jikin ya ci gaba da tabarbarewa.
Likitocin da ke duba shi sun nemi a yi masa hoton kwakwalwa sun kuma dora shi a kan kulawar Likita mai kula da gashin kashi (Physiotherapy), ana cikin shirye shiryen zuwa hoton kwakwalwar ne jikin ya ci gaba da tabarbarewa. Da yake an ce ciwon ajali baya jin magani, zuwa kamar karfe 8 na dare a ranar Alhamis 18 ga watan Mayu Malam Sabo ya ce ga garinku nan. Aka yi jana’izarsa da misalin karfe 10 na safiyar Juma’a 19 ga watan Mayu 2023.
Al’umma da dama suka halarci jana’zar ciki har da wakilai daga gidajen watsa labareai na garin Zariya da kewaye, kamar su ABU FM, Kueen FM, FRCN, Alheri Redio, BON. Sai kuma tawaga daga garin Kwanan Dangoro a karkashin jagorancin Alhaji Nasiru Kafin-Maiyaki, in da ya bayyana marigayi Malam Sabo Ahmad a matsayin mutum mai kokarin sada zumunci, ya ce, “Duk da cewa, Sabo da aiki ne a Abuja amma kusan duk karshen mako yakan kai ziyara Kwanan Dangora don ganin ‘yan uwa da abokan arzik, ya kuma taimaka wa yara da dama masu neman gurbin karatu a makarantun Jihar Kano da yankin Zariya, ‘Za mu yi kewar rasuwasa, muna addu’ar Allah ya gafarta masa ya kuma albarkaici abin da ya bari’’ in ji shi.
Malam Sabo Ahmad mutum ne mai son taimakawa mutane musamman matasa masu hankoron neman guraben karatu, yakan kuma shirya bayar da darussa ga dalibai masu shirin rubuta jarrabawa daban-daban.
Wani abin da wasu da yawa basu sani ba game da Malam Sabo shi ne, duk da Hausa ya karanta a Jami’a amma haziki ne a darusssan lissafi, har ya taba kokarin rubuta littafin lissafi da Hausa don dalibai hausawa su samu saukin fahimtar darasin amma rashin wanda zai tallafa masa yasa abin ya sha ruwa.
A kokarisa na neman na kansa tare da tsayawa da dugadugansa, Malam Sabo ya shiga harkokkin kasuwanci da dama wadanda suka hada da sayar da hatsi, doya, kayan gwari, ‘Electronics da sauransu a garuruwan Abuja, Legas da Zariya wannan harka ta kasuwanci ta sa Malam Sabo sanin mutane da dama, yana kuma da kokarin rike igiyar hulda da abokansa koda kuwa su sun yi sanyi a game da zumuncin da ke tsakainsu.
Harkar jarida kuma ta kai Malam Sabo sassa da dama a arewacin kasar nan, ya kware wajen bayar da labarun abubuwan da ke faruwa a yankuna karkara, inda yake bankado labarun da suka shafi fyade, cin zarafin al’umma, danniya daga masu gari ga talakawa, Malam Sabo kan bi labarai har zuwa kotu don tabbatar da ganin an ba mai hakki hakkinsa, wannan ne ya sa yake rike da shafin ‘Kotu da ‘Yansada na jaridar LEADERSHIP Hausa a zubin Sabon Shafi da muka koma.
Dangantakarsa da sauran abokan aiki, abu ne mai ban sha’awa, don Sabo ba ya raina kowa, in ya shiga ofis sai dai wani dalili zai sa ka ganshi a waje, baya gararamba a harabar ma’aikata, wasu ma’aikata na sashin turanci ba su yi saurin gane Malam Sabo ba saboda yadda yake da karancin shiga cikin mutane.
‘’Malam Sabo ka rasu ranar Alhamis a daren Juma’a a kan haka muke maka kyakyawan zaton samun rahamar Allah, Allah ya gafarta maka, Allah kuma ya kyautata namu in lokaci ya zo” in ji Malam Mamuda wani amininsa.
Shi kuwa Muhammadu Kabir Paki mazaunin Kwanan Dagora wanda tare suka taso da Malam Sabo ya yi addu’a Allah ya gafarta masa. Haka kuma Malam Nasiru Kwana wanda shima amini ne ga Malam Sabo ya ce, sun yi rayuwa na arziki da mutumci da marigayin, ya kuma nemi al’umma su yi koyi da halayarsa ta sada zumunci da sadarkauwa a cikin al’umma, ya kuma yi addu’ar Allah ya shirya masa iyalansa.
A ta bakin dauwansa shakiki, Malam Gadrba Datti, ya ce, ba zai iya kwatanta irin yadda rasuwar Malam Sabo ta taba shi ba, don Sabo ya zame masa tamkar bango wanda ke bashi kariya a dukkan lokutta, ina addu’ar Allah ya gafarta masa, Allah kuma ya bamu hakurin jure rashinsa” in ji shi.
Malam Sabo ya rasu ya bar mata biyu, Maryama da Fatima da yara 10, maza biyar mata biyar, Allah ya gafarta maka ya sa aljanna ta zama makomar ka, Sabo Ahmad Kafin-Maiyaki.
Bello Hamza shi ne Mataimakin Babban Editanmu