Kotun koli ta yi fatali da karar da jami’yyar PDP ta shigar a gabanta kan bukatar da a soke takarar zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu da zababben mataimakin shugaban kasa sanata Kashim Shettima a matsayin ‘yan takarar jami’yyar APC.
Kotun a karkashin jagorancin Alkalai biyar, ta yanke wannan hukuncin ne a yau Juma’a a kan karar da PDP ta shigar, inda kotun ta ce PDP ba ta hurumin shigar da wannan karar tun da ita ba mamba ba ce a Jam’iyyar APC.
PDP dai, ta yi ikirarin cewa, zabo Shettima a matsayin mataimakin Tinubu, ya saba wa sashe na 29, daya a cikin baka da sashe na 33, 35, 84 daya a cikin baka da kuma biyu a cikin baka na dokar zabe ta shekarar 2022 da aka sabunta.
PDP ta kuma yi korafin cewa, zabo Shettima don ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa da kuma takarar kujerar sanata ta Borno ta tsakiya a lokaci daya, hakan ya saba wa doka.