A yau Asabar 27 ga wata ne aka gudanar da bikin kaddamar da littafin “Tambayoyi da amsoshi kan tunanin Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani” cikin harshen Ingilishi a gun bikin baje kolin litattafai na kasa da kasa na Kuala Lumpur a kasar Malaysia.
Za a fitar da littafin cikin harshen Ingilishi ga kasashen duniya masu magana da shi, wanda zai taimaka wa al’ummomin kasa da kasa fahimtar muhimman abubuwan da tunanin Xi Jinping suka kunsa kan tsarin gurguzu mai halayyar musamman na kasar Sin a sabon zamanin da muke ciki, da kara fahimtar hikimomin kasar Sin da alhakin dake rataye a wuyan kasar wato yadda jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ke kokarin inganta gina kyakkyawar duniya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)