Daga shekarar 2020 har zuwa yanzu, wasu kasashen dake nahiyar Afirka da suka hada da Zambia da Ghana sun gamu da matsalar biyan bashi, lamarin da ya janyo hankalin mutanen duniya.
Sa’an nan wasu ‘yan siyasa da kafofin watsa labaru na kasashen yamma sun yi amfani da wannan batu wajen bayyana rashin gamsuwa game da hadin gwiwar Afirka da Sin, inda suka ce rancen da kasar Sin ta samarwa kasashen Afirka “tarkon bashi” ne, wanda ke haifar wa kasashen da matsalar biyan bashi. Amma ko abun da suka fada gaskiya ne?
A hakika, abin ba hakan yake ba. Da farko dai, kasar Sin ba ta cikin bangarorin dake samar da mafi yawan bashi ga kasashen Afirka.
Alkaluman da bankin duniya ya samar a shekarar 2022 sun nuna cewa, cikin bashi na dalar Amurka biliyan 696 da kasashe 49 (wadanda ake iya samun alkalumansu) dake nahiyar Afirka suka ci, bashin da hukumomin kudi na kasa da kasa (irin bankin duniya) da masu bayar da bashi na kasuwanci (misali bankunan kasa da kasa masu samar da rance) suka samar ya kai kashi 3 cikin kashi 4. Hakan ya nuna cewa wadannan hukumomi da bankuna su ne manyan bangarorin dake samar da mafi yawan bashi ga kasashen Afirka.
Ban da wannan kuma, idan an yi kokarin tantance ainihin dalilan da suka haddasa matsalar biyan bashi a kasashen Afirka, za a ga suna da sarkakiya.
Dalili na farko shi ne, mafi yawan kasashen dake nahiyar Afirka suna dogaro kan fitar da ma’adinai da sauran danyun kayayyaki wajen samun kudin shiga. Saboda haka, farashin kayayyakin da suke samar a kasuwannin duniya ya yi tasiri soai kan kudin da kasashen ke samu. Idan kudin da wata kasa ke samu ya yi yawa, to, za ta ci karin bashi. Amma zuwa lokacin da kudin shiga ya ragu, to, kasar za ta fuskanci matsala wajen biyan bashin da ta ci a baya.
Sa’an nan dalili na 2 shi ne, wasu manyan bankunan zuba jari (irin Citi Group) sun samu damar daukar nauyin aikin sayar da takardun bashi da gwamnatocin kasashen Afirka suka samar, inda suke kokarin daga kudin ruwa don neman karin riba. Sai dai lamarin ya zama tushen matsalar biyan bashi, saboda wasu kasashen dake nahiyar Afirka sun riga sun fara yin amfani da mafi yawan kudin da suke samu wajen biyan kudin ruwan bashin da ake binsu.
Dalili na 3 shi ne, bayan shekarar 2016, farashin danyun kayayyaki a kasuwannin duniya ya ragu. Batun nan ya kara da annobar COVID-19, lamari da ya sa dimbin kasashen dake nahiyar Afirka gamuwa da matsalar koma bayan tattalin arziki. Sai dai a wannan lokaci, baitulmalin kasar Amurka ya yi kokarin daga ruwan kudin ajiya har sau da dama, lamarin da ya haifar da karuwar darajar dalar Amurka a kasuwannin kasa da kasa, da sanya dimbin jari kwarara zuwa cikin kasar Amurka da sauran kasashe masu sukuni. Kuma a hannu na daban, batun ya sa darajar kudin kasashen Afirka ta ragu sosai, da haifar musu da karin matsin lamba a fannin biyan bashi.
Ta haka muna iya ganin cewa, bai kamata a dora wa kasar Sin laifi da cewa wai ta sa kasashen Afirka gamuwa da matsalar biyan bashi ba. Amma me ya sa wasu mutanen kasashen yamma suke fadin haka?
Dalili shi ne, domin kasar Sin ba ta son yin biyayya ga kasashen yamma. Kullum kasashe masu sukuni na yammacin duniya suna kallon kansu a matsayin masu tsara ka’idoji a duniya, inda suke bukatar kasar Sin da sauran kasashen da tattalin arzikinsu ke tasowa da su bin tsare-tsarensu wajen ba da bashi. Sai dai kasar Sin na da ra’ayin kanta.
Bayan da muka shiga cikin karni na 21, hukumomin kasashen yamma sun fara rage bashin da suke samarwa kasashen Afirka kai tsaye. A nata bangare, kasar Sin ta lura da yanayin da kasashen Afirka suke ciki na fama da koma bayan tattalin arziki, kuma ta samar da tsarin samar da rance don taimakawa kasashen Afirka raya kasa, bisa fasahohin da ta samu a fannin raya kanta. Inda a wani bangare kasar Sin ta samar da dimbin bashi masu tsawon wa’adi, wadanda ruwansu ba shi da yawa, ga kasashen Afirka kai tsaye, yayin da a bangare na daban, kasar Sin da kasashen Afirka suke hadin gwiwa a kokarin gina kayayyakin more rayuwa a Afirka, bisa yin amfani da rancen da kasar Sin ta samar. Wadannan al’amura sun nuna ra’ayin kasar Sin na kokarin amfanawa kowa yayin da ake hadin gwiwa, da neman samun ci gaban kasa mai dorewa.
Ban da haka, kasar Sin ta halarci shirin kungiyar G20 na baiwa kasashen da suke da matsalar bashi damar dakatar da biyan bashi. A sa’i daya, ba ta dauki dabarar kasashen yamma ta rage bashi bisa sanya wa kasashen Afirka wasu sharuda ba. Maimakon haka, Sin ta fi yin amfani da dabarar dakatar da biyan bashi da kudin ruwa dake tare da bashin, da tsawaita wa’adin bashi ta hanyar shawarwari, wajen taimakawa kasashen da suke da bukata, dabarar da ta yi amfani gami da samar da sakamako mai kyau, yayin da ake kokarin gwada ta.
Kasar Sin tana yin amfani da dabaru da fasahohin da ta samu, yayin da take raya tattalin arzikinta, a fannin hada-hadar kudi, wajen taimakawa kasashen Afirka fid da kansu daga wata da’irar faduwa ta yawan cin bashi amma ba tare da samun ci gaban kasa ba, da dogaro kan matakan yafe bashi, ta hanyar kyautata dabarun yin amfani da kudin da aka samu, da inganta tsare-tsaren aiki.
Sai dai a ganin kasashen yamma, matakin tamkar wata barazana ce ga babakeren da suka kafa a fannin hada-hadar kudi. Bayan da aka tabbatar da cewa tsare-tsaren da kasashen yamma suka samar ba su da amfani wajen taimakawa kasashen Afirka samun ci gaba, kasashe na yammacin duniya na ci gaba da kin amincewa da sabbin dabarun da sauran kasashe suka gabatar. Wannan mataki na taurin kai ya nuna cewa kasashen yamma sun gamu da matsalar rashin karfin gwiwa game da turbarsu ta neman ci gaba. (Bello Wang)