A kwanakin nan ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubutawa wata yarinya yar kasar Bangladesh mai suna Alifa Chin wasika, inda a ciki ya kara mata kwarin gwiwa mayar da hankali kan karatu, da cimma burinta, da ci gaba da sada dadadden zumuncin dake tsakanin Sin da Bangladesh.
Yayin da yake laakari da labarin da Chin ta bayar a cikin wasikar, ya zama misali mai kyau na abokantakar da ke tsakanin kasashen biyu, Xi ya ce tun da dadewa, kasashen Sin da Bangladesh sun kasance makwabta kana abokai na kud da kud, wanda suke mu’amalar sada zumunta, sama da shekaru dubu.
Shugaban kasar Sin ya bayyana cewa, fiye da shekaru 600 da suka gabata, wani ma’aikacin jirgin ruwa na kasar Sin a zamanin daular Ming mai suna Zheng He, ya yi bulaguro zuwa kasar Bangladesh har sau biyu, inda ya dasa dankon zumunci tsakanin al’ummomin kasashen biyu.
Xi ya bayyana fatan cewa, Chin za ta yi amfani da shekarun kuruciyarta yadda ya kamata, da yin karatu tukuru don ganin burinta ya zama gaskiya, yana mai cewa daga nan ne kuma za ta iya ba da gudummawa ga danginta, da al’umma, har ma ta yiwa kasarta hidima. (Mai fassarawa: Ibrahim)