Ƙungiyar Fafutukar Tabbatar da Ci Gaban Nijeriya ta ‘Grassroots Mobilizers For Better Nigeria Initiatiɓe (GMBNI)’ ta karrama ma’aikacin Rukunin Kamfanonin LEADERSHIP, Rabiu Ali Yusuf da wasu mutane haziƙai da lambar yabo bisa gudunmawarsu ga ci gaban al’umma.
Kwamitin gudanarwa na ƙungiyar na ƙasa ƙarƙashin ingantaccen jagorancin Ambasada Dakta Fatima Mohammed Goni fgau, shugabar ƙungiyar ta ƙasa ne ya yi zama na musamma domin zaƙulo haziƙan mutane inda ta amince da girmama su da lambar yabo don nuna goyon baya, sadaukarwa, da kuma gagarumar gudunmawar da suke bayarwa ga ƙungiyar.
Daga cikin waɗanda suka lambar yabon akwai ‘yan jarida waɗanda an karrama su ne bisa cancanta da jajircewarsu a ayyukansu.
Da take jawabi a yayin bayar da lambobin yabon Ambasada Fatima Muhammad Goni ta ce, waɗannan jama’a da muka a ƙarƙashin ƙungiyar da nake shugabanta (GMBNI), mun karrama su ne saboda jajircewarsu a wannan ƙungiya wajen ganin ta cimma burin da ta sa a gaba.
Mun yi abubuwa da dama wanda kuma duniya ta gani, kuma muna gode wa Allah da ya kawo mu wannan lokaci, ina yi wa kowa fatan alheri da addu’ ar Allah ya zaunar da ƙasarmu lafiya. Ga dai jerin sunayen mutanen da wannan ƙungiya ta karrama da lambar girma kamar haka.
1Jodah Makinta, Darakta kuma Kodinetan tsare-tsare na Jihar Nasarawa. Sai kuma Kwamared Salihu Abdulhamid Dembos, Darakta Janar na Gidan Talabijin na ƙasa NTA. Akwai Lawan Modu Bama, Mataimaki na musamman ga Suhgaba kuma wacce ta kafa ƙungiyar kan ayyuka na musamman, akwai Nancy Habila Mai Ba Da Shawara ta Musamman ga Shugabn ƙungiyar ta ƙasa.
Sharhabil Iliya, Mataimaki na Musamman ga shugabar ƙungiyar ta ƙasa akan harkokin yaɗa labarai. John Ola Zach, Shugaban masu ɗaukar hoto ga shugaban ƙunyar ta ƙasa.
Injiniya.Abdullahi Aliyu. Ambasada Ahmed Umar Bolori, Mataimakin Shugaban Makranta. Lt Col. SJ Dibal, Daraktan Tsaro da Bayar da Bayanan Sirri.
Sauran su ne, Barista Umar Alhaji Bukar, Daraktan Harkokin Shari’ a. Hajiya Hassana Shuaibu Abbas, Kodineta ta Abuja, Abbas Rufai, kodineta na Jihar Jigawa. Gidan Talabijin na Liberty. Timothy T. Kosuga Mai Ba Da Shawara na musamman ga shugaban ƙungiya ta ƙasa a fannin fasaha.
Har ila yau shi ma Musa Aminu, ya samu lambar yabon haziƙin ɗan jarida da Injiniya Kamilu Nasiru Abubakar, Mai Ba Da Shawara na ƙasa.
Modu Bukar, Mai Ba Da Shawara na Musamman ga shugabar ƙungiyar kan al’amuran ilimi. Muhammad Hassan Umar, Mataimaki na Musamman ga Shugabar ƙungiyar akan Kula da harkokin baƙi.
Har ila yau akwai Abdulkarim Kayama Abdullahi, Kodineta na Jihar Yobe, Hajiya Medina Dauda Nadabo, Kodineta kuma jami’a a Shirin da Aliyu Tanko, Shugaban Sashen Hausa na BBC, da Uwaisu Abubakar Idris, Wakilin Gidan Rediyo da Talabijin na Deutche Welle Abuja, sai Apostle B.O Anana, Mai Ba Da Shawara na ƙasa.
Sauran su ne Alhaji Aliyu Musa Turaki, Mai Ba Da Shawara Na ƙasa. Fatima Damagudu Ibellogo, Kodineta na Jihar Binuwai. Hon. Aminu Mohammed Makko, Kodineta na Jihar Gombe. Bwalmo Dubi Abraham, Kodinetan Jihar Adamawa. Suleiman Ibrahim Ali, Kodinetan Jihar Kaduna. Kwamared Mahmood Yayale Nasir, Tsohon Kodinetan Jihar Bauchi.
Haka nan an karrama Dakta Aminu Safana Aliyu, Kodinetan Jihar Katsina. Dakta Abasiama Isidore, Kodinetan Jihar Akwa Ibom. Yusuf Sani Abdullahi, Kodinetan Jihar Filato. Hajiya Maryam Eli Pawa. Kasim Jodah Awi, Mai Ba Da Shawara ga Shugabar ƙungiyar Kan Harkokin Matasa. Muktar Danmaje, Kodinetan a yankin Kudu maso Yamma. Rabiu Ibrahim Abdullahi, Mataimakin Daraktan Tsare-tsare. Zubairu Babangida, Mataimakin Shugaban Masu ɗaukar Hoto ga Shugabar ƙungiyar ta ƙasa
Mahmud Abubakar, Mai Ba Da Shawara na Musamman ga Shugabar ƙugiyar na ƙasa Akan Al’ amuran Gida. Abdullahu Ayuba Ansari, Mai Sanya Ido. Bala Mbaya, Jami’in sa kai. Aisha Umar Jami’ar Sa kai. Lawal Mohammed Abdul (Late Lawal Family), Kodinetan Osun. Mardiyya Adamu (Iyalin Marigayi Auwal, Shugaban Direbobin Shugabar ƙungiya na ƙasa.
Kazalika, ƙungiyar ta karrama manya-manyan malaman tsangaya da suka ba da gudunmawa wajen addu’ o’ i ba dare ba rana, a ƙarƙashin jagorancin Ambsada Fatima Muhammad Goni Shugabar ƙungiyar ta ƙasa kuma wacce ta kafa ƙungiyar.