Dakarun sojin Hadin guiwa ta sojoji da ‘yan banga (OPHK) sun kashe wasu da ake zargin ‘yan ta’addan ISWAP ne su 11 a wani hari da sojojin suka kai a cikin dajin Sambisa da ke jihar Borno.
‘Yan ta’addan sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da jami’an suka samu rahoton sirri sannan suka farmake su a tsakanin ranar 31 ga watan Mayu zuwa 4 ga watan Yunin 2023 a maboyar ‘yan ta’addan da ke cikin kananan hukumomin Damboa da Chibok.
Majiyoyin leken asiri na kusa da Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya, kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, sun bayyana cewa, sojojin sun kai mai ‘yan ta’addan hari ne kuma sun yi nasara tare da tarwatsa wasu maboyar ‘yan ta’addan a Bale, Tirke, Mandari, Molgoi, Bego, Yarwa da Ngurna.
Majiyoyin sun sake shaida cewa, an samu nasarar kwato wasu makamai da alburusai da sauran kayan yaki a yayin farmakin da sojojin hadin guiwar suka kai.