Gobe ranar teku ce ta kasa da kasa karo na 15, babban taron MDD karo na 63 ya tsai da ranar 8 ga watan Yunin kowace shekara ranar teku ta kasa da kasa, don jan hankalin duniya muhimmancin kiyaye teku, wanda ke da babbar ma’ana ga bunkasuwar al’umma.
Amma a abin takaici ne, albarkacin wannan muhimmiyar rana, kasar Japan har yanzu tana kare aniyarta ta zuba ruwan dagwalon nukiliya ta tashar nukiliya ta Fukushima cikin teku bisa son kanta. Kwanan nan, kafar NHK ta kasar Japan ta ba da labarin cewa, an riga an fara zuba ruwan teku cikin bututun da ruwan dagwalon nukiliya zai bi a Fukushima.
Shirin nan na Japan ya jawo suka daga gida da ma waje, sai dai gwamnatin Japan ta yi ta neman wanke kanta ta kowa ce hanya.
Gwamnatin Japan ta ce ruwan dagwalon ba zai kawo illa ga muhallin teku ba, amma ko hakan gaskiya ne? A hakika, ruwan dagwalon tashar Fukushima na kunshe da sinadaran nukiliya masu guba sama da 60. Kamfanin samar da wutar lantarki na Tokyo ya ba da wani rahoto a ran 5 ga wata cewa, an gano abin tiriri na Cesium a jikin nau’in kifin da aka kama a gulf din tashar nukiliya ta Fukushima, yawansa ya ninka sau 180 bisa na ma’aunin da aka tanada.
A sa’i daya kuma, igiyar ruwa a wannan wuri na da karfi matuka, matakin da ya sa idan an zuba ruwan dagwalon nukiliya cikin teku, zai yadu zuwa duk fadin tekun duniya a cikin shekaru 10 masu zuwa, abin da zai kawo babbar illa ga muhallin teku da lafiyar jikin Bil Adama.
Bisa dokar kasa da kasa, ruwan dagwalon nukiliya na Fukushima shara ce, dole ne a ajiye su a maimakon zuba su a cikin teku. Misali a tashar samar da wutar lantarki ta amfani da karfin nukiliya ta kasar Faransa, an kafa cibiyar adana sharar da tashar ke samarwa, matakin da ya fi dacewa.
Gwamnatin Japan ta fitar da shirye-shirye da dama game da yadda za a yi da ruwan dagwalon nukiliya na tashar Fukushima tun daga shekarar 2013, amma daga karshe ta zabi wannan shiri maras imani don yin tsimin kudi da kare kanta.
Shin ko gwamnatin Japan ba ta da isashen kudi? A’a, ba ta da imani ne! Matakin ta zai kawowa muhalli matukar barazana, har ma ya illata makomar Bil Adama baki daya. (Mai zana da rubuta: MINA)