Batun da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabinsa na rantsar da shi cewa gwamnatinsa ba za ta ci gaba da biyan kudin tallafin mai ba a Nijeriya ya sa al’umma sun sha jinin jikinsu game da kamun ludayinsa.
Har yanzu ana ci gaba da mayar da martani a kan abin da shugaban ya ayyana daga sassa daban-daban, ciki har da barazanar zuwa yajin aikin da kungiyoyin kwadago suka dakatar bayan tattaunawa da suka yi da bangaren gwamnati.
- ‘Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Da Ya Yi Wa Yarinya Fyade, Ya Jefar Da Ita A Otal
- Hajjin 2023: NAHCON Ta Ware Wa Maniyyata Kwanaki 5 Don Zama A Madina
Bayan bayyanar dogayen layuka a gidajen sayar da man fetur, saboda masu ababen hawa sun shiga razani saboda rashin sanin tabbas na abin da zai biyo baya, sai ga shi layukan sun bace yayin da aka kara kudin lita daga Naira 195 zuwa tsakanin Naira 480 zuwa Naira 570, wanda hakan ke nuna an yi karin kashi 175.
Yayin da yawancin ‘yan Nijeriya suka nuna goyon bayansu ga cire tallafin man amma kuma sun nuna tsoronsu da rashin amincewa da lokacin da aka yi sanarwar da kuma yadda aka yi sanarwar gaba daya.
Babbar matsalar da musamman kungiyoyin kwadago suka nuna shi ne, da ya kamata a fadada tattaunawa da bangarorin al’umma a kan shirin, sannan a shirya sosai a kan yadda za a fuskanci matsalolin da za su biyo bayan cire tallafin, musamman halin da talakwa da suke zaune a yankuna karkara za su shiga sakamakon karin farashin na fetur. Mun fahimci wannan korafi nasu, musamman in aka lura da yadda sanarwar ta taimaka wajen kara hauhawar farashin kayan masarufi duk da halin da ake ciki na tsadar kayyakin amfanin al’umma na yau da kullum.
Amma kuma in za a fuskanci gaskiya, ya kamata a fahimci cewa, kasar na cikin wani hali na rashin kudi, ba zai yiwu a ci gaba ba da daukar nauyin tallafin mai ba, musamman ganin yadda kudin tallafin ya tashi daga Naira Biliyan 257 a shekarar 2006 zuwa Naira Tiriliyan 4.4 a shekarar da ta gabata.
Ya zuwa ranar 29 ga watan Mayu, lokacin da Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin gaba daya, dokar alkinta albarkatun man fetur ta (PIA) ta riga ta cire tallafin kusan wata 15 da suka gabata amma gwamnatin shugaba Buhari ta san dabarar da ta shigar da Naira Tiriliyan 3.36 cikin kasafin kudin shekarar 2022 don ta tsawaita lamarin tallafin zuwa watan Yuni na shekarar 2023.
A ranar 26 ga watan Janairu na shekarar da ta gabata, LEADERSHIP ta ruwaito cewa shawarar tsohon Shugaban kasa Buhari na dakatar da aiwatar da dokar PIA da watanni 18, musamman shawararsa ta kin janye tallafin man fetur, wani salo ne na yi wa wanda zai gaje shi turin-je-ka-ka-mutu.
Shawarar Shugaban kasa Tinubu ta kawo karshen tallafin mai, abu ne da ya fada tun kafin a yi zabe, shawara ce mai kyau, mun yi imanin ya yi abin da ya kamata.
Idan za a iya tunawa manyan ‘yan takarar shugabancin kasar nan kamar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na jami’iyyar PDP da Peter Obi na jam’iyyar LP a yayin yakin nema zabe su ma sun yi alkawarin za su kawo karshen bayar da tallafin mai in har suka zama shugaban kasa. Daga baya Mista Obi, ya rinka kwatanta lamarin tallafin man da wata ‘shiryayyiyar zamba’ a tattaunawar da aka rinka yi da shi.
Muna tare da su a wannan ra’ayin. Badakalar tallafin mai da kamfanoni 5 tare da NNPC suka yi a shekarar 2006, daga bisani ta gawurta inda a shekarar 2011 aka samu kamfanoni 140 da hannu dumudumu a badakalar da ta kai ta fiye da Dala Biliyan 6.8 wanda aka tafka a cikin shekara 3, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Wasu jami’an gwamnati da aka samu da hannu a ciki na ci gaba da fuskantar shari’a a kotuna, muna nan mun zura ido zuwa ranar da za a hukunta su.
Ba zai yi wu a ci gaba da tafiyar da harkoki a haka ba. Wata kungiya ma isa ido mai zaman kanta mai suna ‘Independent financial watchdogs’, ta bayyana cewa, in har aka ci gaba da tallafin zuwa karshen shekarar 2023, zai kai naira Tiriliyan 6.72 wanda hakan ke nuna ya kai kashi 3 na kasafin kudin shekarar 2023. Ga kasa da ta rika ta ci bashin da za a ci gaba da biya har jikoki ya nuna kenan za a ci gaba da cin bashi don biya bashin tallafin mai, yadda Buhari ya ci tulin bashi ga Nijeriya abin takaici ne kwarai da gaske.
Bayan shalkwatar Nijeriya Abuja da shalkwatar kasuwancin Nijeriya Legas wasu garuruwa kadan ke sayen man fetur a kan farashin da aka kayyade na naira 195, ‘yan Nijeriya a wasu sassan kasa sun dade suna sayen man da tsadar gaske, tun daga tsakanin N285 zuwa Naira 400 a kan lita daya.
Wannan jaridar na sane da irin halin matsin da al’umma suka shiga sakamakon tashin farashin kayan abinci da kudin sufuri da kuma halin da masu kananan masa’anantu suka shiga a kokarin sayen fetur din da za su zuba a kananan ‘Janaraito’ don ci gaba da sana’o’insu.
Mun fahimci halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman ganin yadda wasu jami’an gwamnati suka yi facaka da dukiyar al’umma tare da hadin kan ‘yan siyasa a tsawon shekaru. Muna sane da ciwon da ‘yan Nijeriya ke ji, musamman mazauna yankuna karkara da za su rinka tunanin wai shin mene ne ake amfana da shi a Nijeriya?
Ta yaya talakawa ke amfana da tallafin man fetur, musamman ganin kungiyar nan mai zaman kanta mai suna ‘PricewaterhouseCoopers (PwC)’ ta bayyana cewa, kashi 40 na ‘yan Nijeriya ke amfani da man fetur wanda ke nuna kashi 3 ke nan na tallafin man da ake bayarwa. Mun yi imanin hanyar da gwamnati za ta sauya salon al’umurra musamman a rayuwar al’umma shi ne ta sauya yadda take gudanar da harkokin al’umma/gwamnati, ta kuma yi haka a cikin sauri da gaggawa. Hakan kuma zai hada da daukar matakai masu zafi.
A rahoton ta na kwana-kwanan nan, PwC ta bayyana cewa, cikin alfanun cire tallafin mai sun hada da rage cin bashi da kuma kara zuba jari ga bangarori masu muhimmanci ga rayuwar al’umma zai kuma kara darajar Naira a kasuwannain duniya. Tun da aka cire tallafin kalanzi da bakin mai a shekarar 2016, farashinsu ya daidaita an kuma samu yawaltuwar su a fadin Nijeriya.
Haka kuma in har ana son a kawo karshen babakeren da kamfanin NNPC ya yi wajen hana kamfanoni masu zaman kansu su wala wajen gudanar da harkokin samar wa da al’umma man fetur a kasuwannin Nijeriya, dole a samar da wasu dokoki da za su taka wa NNPC birki.
A kan yadda za a tabatar da man fetur ya isa dukkan lungunan kasar nan ba tare da wahala ba dole shugaban kasa ya yi shawarar yadda zai yi da matatun man fetur na gwamnatin tarayya wadanda suka laukume fiye da Dala Biliyan 25 a cikin shekara 20 ba tare da sun aiwatar da komai ba. A rahoton jaridar ‘BusinessDay’ ta ranar 14 ga watan Satumba 2021 ta bayyana cewa matatun man sun dauki ma’aikata fiye da 1,586 wanda albashin su ya kai Dala Biliyan 69!
Ya kamata gwamnati da sake duba shirin nan na samar da iskar gas wato ‘National Gas Edpansion Programme (NGEP)’ wanda gwamnatin Buhari ta fara inda aka shirya samar tare da amfani da iskar gas maimakon fetur a sannu a hankali, bayani ya nuna cewa, iskar gas na da sauki, baya kuma cutar da muhalli.
Hakan zai rage dogaro da ake yi ga man fetrur. A lokacin da NNPC ta kaddamar da shirin a shekarar 2020, ta bayyana cewa, zuwa shekarar 2021 za ta samar da motoci fiye da miliyan 1 masu amfanin da iskar gas ga ‘yan kasa amma daga dukkan alamu shirin ya kwanta dama duk kuwa da fiye da Naira Biliyan 250 da Babban Bankin Nijeriya ya zuba a ciki.
Akwai bukatar a gaggauta samar da tallafi a bangaren motocin haya da al’uimma ke amfani dasu, harkar noma da bangaren kanana da matsaikatan masana’antu, wanda suna daga cikin bangaren da suka fi dandanawa.
A bangaren harkar sufuri kuwa gwamnati na iya bayar da tallafi na musamman ga masu motoci da aka kiyasta sun kai miliyan don su samu sauki, ta haka kuma sauran al’umma za su amfana suma, a rage matsalolin da suke fuskanta sakamakon cire tallafin da aka yi.
Babban kuskure a kawar da kai daga al’umma da suke da korafi wadanda ake ganin ana nuna musu wariya. Akwai bukatar gwamnati ta samar da hanyoyin tattauanawa tare da nemo mafita ta yadda kowa zai san ana yi da shi, a kuma sake farfado da fata a tsakanin al’umma.
Ya kuma kamata al’umma su samar wa da kansu hanyoyin ci gaba da rayuwa ba tare da mastala, musamman ganin cewa, cutar korona ta koya mana kumajin dogaro da kai, mu fuskanci gaskiyar halin da ake ciki don mu haye ba tare da mun cutu sosai ba.
Daga karshe muna murna da labarin da muka ji na cewa, shugaban kasa Tinubu na shirin karin albashin ma’aikata da sake duba ka’dojin aiki a Nijeriya. Don tabbatar da an amfana, ya kamata gwamnatin tarayya da na jihohji su gaggauta aiwatar da shirin su kuma sa ido don ganin dukkan ma’aikatu da hukumomin gwamnati sun aiwatar da karin albashin don al’umma gaba daya su amfana.
Duk wani abn da ya gaza haka za iyi kama ne zuba fetur a cikin wutar data kama gadan-gadan.