Shugaban kungiyar ‘yan banga a jihar Neja, Yarima Nasiru Manta yayi barazanar dakatar da aikin kungiyar na yaki da masu garkuwa da mutane da suka addabi mutanen karkara da hanyoyin jihar da ‘yan daba da suka addabi cikin garin Minna.
Shugaban ya bayyana hakan ne ga manema labarai jim kadan bayan rundunar ‘yan sanda ta sako shi bayan tsare shi kwana daya da yini daya a hedikwatar rundunar ‘yan sandan.
Manta, ya cigaba da cewar wasu marasa kishin jiha ne suka kai korafi ga rundunar ‘yan sanda bisa zargin sa da cewa wai yana wuce gona-da-iri wajen tsare masu laifi sama da kwana uku.
Manta ya karyata zargin, Yace ba ma tsare masu laifi, domin kwamishinan ‘yan sandan da ya wuce CP Adamu Usman ne ya horar da mu bisa umurnin maigirma gwamna Abubakar Sani Bello saboda yaki da ‘yan ta’addan da suka addabi jihar, mun samu nasara sosai da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro na tarwatsa sansanin ‘yan ta’adda masu garkuwa da jama’a, da kuma matasa ‘yan daba dake addaban mazauna cikin garin Minna.
Yarima Nasiru Manta, yace akwai wani dan siyasa da ke gidan gwamnatin jiha, da muka kama surukinsa cikin ‘yan daba, saboda kusancin sa da gwamnati sai ya garzaya hedikwatar rundunar ‘yan sanda ya baiwa kwamishinan ‘yan sanda rahoton karya.
Ba tare da bata lokaci ba kwamishinan ‘yan sanda ya gayyace ni, nan take na amsa gayyatar sa, ba tare da bata lokaci ba ya umurci bangaren binciken laifuka na rundunar da su tsare ni.
Bayan an tsare ni kuma ‘yan daban suka cigaba da aika-aikar na su inda kwamishinan kananan hukumomi da masarautu da tsaron cikin gida, a daren washe gari cikin bacin rai ya umurci kwamishinan ‘yan sanda ya sake ni, ba tare da rubuta beli ko wani kwakkwaran bincike da safe aka sake ni.
Yanzu na umurci dukkanin mambobin mu da ke aiki tare da ni da su dakatar da aikin, mu bar ‘yan sanda su yi aikin su. Kila idan gwamna na son Aikin zai gayyaci dukkanin bangarorin dan jin bahasin abinda ya kai ga tsare ni. Ba sata na yi ba, laifina kawai kama masu laifi don suna da uwa a gindin murhu.
Ko a yammacin asabar zuwa wayewar lahadi ‘yan dabar sun farwa junansu a yankin Kwangila zuwa Limawa, da nan bangaren Limawa zuwa Obasanjo complex kuma na shaidawa yara cewar kar wanda ya fita.
Yunkurin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda dai ya cutura, domin wayar kakakin rundunar ‘yan sandan ba ta zuwa.