• English
  • Business News
Friday, November 7, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamnan Zamfara Ya Kai Ziyarar Jaje Tsafe, Ya Nanata Muradin Magance Matsalar Tsaro

by yahuzajere
2 years ago
zamfara

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a yau Alhamis ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na magance matsalar tsaron da ke addabar jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ziyarar jajantawa da ya kai fadar Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa bisa harin rashin imanin da ‘yan bindiga suka kai garin.

Wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce Gwamnan ya je Tsafe ne don ya yi jaje, ya kuma tabbatarwa jama’a ƙudurinsa na yi wa tufkar hanci.

  • Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 12 Ga Watan Yuni, Ranar Hutu

Gwamnan ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da aka samu a wasu yankuna ciki har da Tsafe.

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

“Na kawo wannan ziyara ne domin jajantawa masarauta da al’ummar ƙaramar hukumar Tsafe bisa harin da ‘yan bindiga suka kai musu.

“Ina so na tabbatarwa da mai martaba da al’ummarmu cewa tsaro shi ne abu mafi muhimmanci ga gwamnatinmu, dalilin da ya sa nake aiki da sauran ɓangarorin tsaro don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.

“Ni da wasu gwamnoni mun samu damar ganawa da Shugaban Ƙasa Tinubu a Abuja, kuma na bijiro mishi da maganar rashin tsaro a Zamfara. Shugaban ƙasan ya tabbatar da zai bani cikakken goyon baya. Don haka ne ma na sake neman alfarmar sake zaunawa da shi don mu tattauna wannan matsalar.

“Lokacin da aka sanar da ni labarin wannan hari na ‘yan bindiga a Tsafe, a take na kira jami’an tsaro, inda suka kai ɗaukin gaggawa.

“Yayin da gwamnati ke aiki don magance wannan matsala, ina kira ga al’umman Jihar Zamfara da su ƙarfafa yin addu’a ga wannan jiha. Muna matuƙar buƙatar goyon baya a wannan al’amari.”

Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, a nashi jawabin, ya roki Allah Ya yi jagora ga Gwamna Lawal, musamman la’akari da irin jajircewarshi don ganin an samu zaman lafiya a Zamfara.

“Ina so na yi godiya tare da jinjina ga Gwamna bisa wannan ziyarar jaje da ya kawo mana. Ba zan iya ɓoye farin cikina ba, saboda wannan shi ne karo na farko da aka samu Gwamna ya tako don jajanta mana kan harin ‘yan bindiga.

“Haka nan kuma dole ne na jinjinawa irin taimakon gaggawa da muka samu daga Gwamna, wanda ya dakile yiwuwar dawowar ‘yan bindigan. Za mu ba wannan sabuwar gwamnati duk wata gudummawa da take buƙata a wannan shiri nata na kawo ƙarshen matsalar Zamfara”, in ji Sarkin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT
Manyan Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 
Manyan Labarai

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya
Labarai

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Next Post
Cire Tallafin Mai Ya Dace, Amma A Gaggauta Saukaka Wa Al’umma

Cire Tallafin Mai Ya Dace, Amma A Gaggauta Saukaka Wa Al’umma

LABARAI MASU NASABA

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

An Yi Taron Kaddamar Da Tsarin Kawancen Kafafen Watsa Labarun Kasashe Masu Tasowa Da Dandalin Yada Labarai Na Bidiyo Karo Na 13 A Xi’an

November 6, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST

November 6, 2025
Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

Baje Kolin CIIE Ya Bayar Da Tabbaci Ga Duniya

November 6, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A  FCT

November 6, 2025
Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

Manufofin Sin Na Yaki Da Sauyin Yanayi: Gani Ya Kori Ji

November 6, 2025
Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

Shugaba Xi Ya Jaddada Bukatar Gina Ingantaccen Yankin Ciniki Cikin ’Yanci Na Tashar Ruwa Ta Hainan

November 6, 2025
Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

Amurka Ta Yi Barazanar Ƙwace Kadarorin Ƙungiyoyin Makiyaya A Nijeriya 

November 6, 2025
A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu

November 6, 2025
Gwamnatin tarayya

Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu

November 6, 2025
Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

Bikin Baje Kolin CIIE: Da Abokin Daka Ake Shan Gari

November 6, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.