Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, a yau Alhamis ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na magance matsalar tsaron da ke addabar jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wata ziyarar jajantawa da ya kai fadar Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa bisa harin rashin imanin da ‘yan bindiga suka kai garin.
Wata sanarwar manema labarai da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce Gwamnan ya je Tsafe ne don ya yi jaje, ya kuma tabbatarwa jama’a Æ™udurinsa na yi wa tufkar hanci.
Gwamnan ya bayyana damuwarsa kan hare-haren da aka samu a wasu yankuna ciki har da Tsafe.
“Na kawo wannan ziyara ne domin jajantawa masarauta da al’ummar Æ™aramar hukumar Tsafe bisa harin da ‘yan bindiga suka kai musu.
“Ina so na tabbatarwa da mai martaba da al’ummarmu cewa tsaro shi ne abu mafi muhimmanci ga gwamnatinmu, dalilin da ya sa nake aiki da sauran É“angarorin tsaro don tabbatar da wanzuwar zaman lafiya.
“Ni da wasu gwamnoni mun samu damar ganawa da Shugaban Ƙasa Tinubu a Abuja, kuma na bijiro mishi da maganar rashin tsaro a Zamfara. Shugaban Æ™asan ya tabbatar da zai bani cikakken goyon baya. Don haka ne ma na sake neman alfarmar sake zaunawa da shi don mu tattauna wannan matsalar.
“Lokacin da aka sanar da ni labarin wannan hari na ‘yan bindiga a Tsafe, a take na kira jami’an tsaro, inda suka kai É—aukin gaggawa.
“Yayin da gwamnati ke aiki don magance wannan matsala, ina kira ga al’umman Jihar Zamfara da su Æ™arfafa yin addu’a ga wannan jiha. Muna matuÆ™ar buÆ™atar goyon baya a wannan al’amari.”
Sarkin Tsafe, Alhaji Muhammadu Bawa, a nashi jawabin, ya roki Allah Ya yi jagora ga Gwamna Lawal, musamman la’akari da irin jajircewarshi don ganin an samu zaman lafiya a Zamfara.
“Ina so na yi godiya tare da jinjina ga Gwamna bisa wannan ziyarar jaje da ya kawo mana. Ba zan iya É“oye farin cikina ba, saboda wannan shi ne karo na farko da aka samu Gwamna ya tako don jajanta mana kan harin ‘yan bindiga.
“Haka nan kuma dole ne na jinjinawa irin taimakon gaggawa da muka samu daga Gwamna, wanda ya dakile yiwuwar dawowar ‘yan bindigan. Za mu ba wannan sabuwar gwamnati duk wata gudummawa da take buÆ™ata a wannan shiri nata na kawo Æ™arshen matsalar Zamfara”, in ji Sarkin.