Alkaluman da masana’antun kera motoci na kasar Sin suka fitar ya nuna cewa, cinikayyar motocin fasinja kirar kasar Sin ta karu da kashi 37.6 bisa 100 a watan Mayu idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
A cewar kungiyar masu kera motoci ta kasar Sin, kimanin motocin fasinja kirar gida miliyan 1.1 aka sayar da su a kasar Sin a watan da ya gabata, wanda ya kai kashi 53.6 na dukkan motocin fasinja da aka sayar a kasar.
Bayanai na nuna cewa, a cikin watanni biyar nShugabar Kasar Honduras Ta Fara Ziyara a Kasar Sina farkon wannan shekara, tallace-tallacen irin wadannan motocin ya karu da kashi 22.7 cikin 100 a shekara zuwa motoci miliyan 4.78.
Kungiyar ta ce, kasuwannin wadannan motocin sun rika fadada akai-akai a cikin shekarar 2023. (Mai fassarawa: Ibrahim)