Shugaban Kungiyar masu sana’ar kiwon Kajin Gidan Gona reshen jihar Kaduna PAN Musa Bala ya bukaci masu sana’ar da ke a daukacin fadin kasar nan, musamman a jihar Kaduna da su dinga tuntubar kwararrun Likitocin Kajin kiwon Kajin Gidan Gona a yayin da Kajin basu da lafiya.
Bala ya bayar da wannan shawarar ce a hirarsa da Leadership Hausa a Kaduna jim kadan bayan tashi daga taron bita na kwana daya da aka shirya wa wasu daga cikin masu sana’ar da ke a jihar, inda ya kara da cewa, ta hanyar tuntubar ce kawai, za su kauce wa yin asara a cikin sana’ar ta kiwon.
Shugaban ya ci gaba da cewa, kungiyar ta jima ta na ilimantar wa da kuma fadakar da masu sana’ar kan mahimmancin tuntubar kwararrun Lokitocin kiwon Kajin Gidan Gona idan Kajin sun kamu da wata rashin lafiya, musamman don gudun kar su dinga yin asara a cikin sana’ar ta su.
Ya yi nuni da cewa, idan ba sa tuntubar kwararrun Likitocin kiwon Kajin Gidan Gona, tamkar suna jefar da jarinsu da suka zuba a cikin sana’ar ce, inda kuma ya bukci su ma kwararrun Likiticin da su dinga yin aiki mai kyua a inda aka bukace su .
” Kungiyar mu ta jima ta na ilimantar wa da kuma fadakar da masu sana’ar kan mahimmancin tuntubar kwararrun Lokitocin kiwon Kajin Gidan Gona idan Kajin sun kamu da wata rashin lafiya, musamman don gudun kar su dinga yin asara a cikin sana’ar ta su.”
” Idan ba sa tuntubar kwararrun Likitocin kiwon Kajin Gidan Gona, tamkar suna jefar da jarinsu da suka zuba a cikin sana’ar ce, inda kuma ya bukci su ma kwararrun Likiticin da su dinga yin aiki mai kyua a inda aka bukace su .”
Da yake yin tsokaci kan irin gudunmawar da masana’atar take bayarwa a kasar nan Bala ya ce, masana’antar Kiwon Kajin duk da kalubalen da take fusknata, ta na bayar da gagarumar gudunmawa, musamman wajen daukar miliyoyin ‘yan Nijeriya aiki kai tsaye da kuma sauran miliyon ‘yan kasar da take dauka ban a kai tsaye ba , inda ya sanar da cewa, masana’atar na kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan.
“Duk da kalubalen da take fusknata, ta na bayar da gagarumar gudunmawa, musamman wajen daukar miliyoyin ‘yan Nijeriya aiki kai tsaye da kuma sauran miliyon ‘yan kasar da take dauka ban a kai tsaye ba , inda ya sanar da cewa, masana’atar na kuma samar da wadataccen abinci a kasar nan. “
Shi ma a hirarsa da Leadership Hausa bayan taron, wani kwarararren Likitan Kajin Gidan Gona Dakta James Baba Wageti ya goyi bayan ra’ayin shugaban kungiyar ta PAN, inda ya ce, duk da cewa, akwai tsada wajen dauko Likitocin na Kajin Gidan Gona da zasu duba lafiyar Kajin, amma ya bayar da shawara a dinga yin tuntubar, musamman don su kauce wa tabka asara.
A cewarsa, wasu masu kiwon Kajin Gidan Gona a kasar nan sun shiga sana’ar ce a makance, inda ya yi nuni da cewa, akwai bukatar su fahinci yadda nauyin Kajin yake kasance wa tare da kuma sa ido a kan Kajin.
Dakta James ya kuma shawarci masu kiwon kiwon Kajin na Gidan Gona da ke a kasar nan da su gabatar da rokonsu ga Majalisar Tarayyar kasar don a gabatar da kudurin da zai tsaftace fannin, musamman don a magance mutuwar Kajin Gidan Gona a kasar nan.
Ya yi nuni da cewa, yawancin Gidajen Gidan Gona da ake kiwata Kajin don neman riba, na kusa-kusa da juna ne, inda y ace kamata ya yi Gidajen Gidan Gonar su kasance nesa da kilomita daya don a kare Kajin daga harbin kwayoyin cuta.
Taron bitar mai taken: “ Hanyar Yin Kiwon Kaji Mai Ingancin”, kamfanin Betor Libe stocks Solutions da hadakar kamfanin Adamore ne suka shirya taron.