Har yanzu wasu manoman da ke a jihar Beninew ba su fara yin shuka ba, musaman saboda jinkirin da aka samu na saukar Ruwan sama a wasu sassan jihar.
Manoman wadada suka sa ran fara samun Ruwan saman tun a cikin watan Afililun da ya wuce, don su fara yin shukar sun koka kan jinkirin na saura Ruwana saman.
- An Bude Taron Dandalin Hamadar Taklimakan A Birnin Korla Na kasar Sin
- Manchester City Ta Lashe Gasar Zakarun Turai
Rahotanni sun bayyana cewa, akasarin manoman sun yi sharer gonakan su, amma Ruwan saman bai fara sauka ba.
Daya daga cikin manoman mai suna John Zuzu da ke a yankin Tse-Nyon, a a cikin garin Makurdi John Zuzu, ya koka kan jinkirin da aka samu na saukar Ruwan saman kan lokaci.
A cewrsa, tun daga ranar 14 ga watan Mayun, 2023, bai iya fara yin shuka Masara a gonarsa ba, saboda fari.
Zuzu ya bayyana cewa, tun da aka samu saukar Ruwan sama sau uku a damainar bana a yakin na Tse-Nyon, har zuwa yanzu ba a kara samun saukar wani Ruwan sama ba.
Shi ma wani manomin a karamar hukumar Otukpo a jihar ta Binewe mai suna Paul Echioda, ya sanar da cewa, shi manomin Doya ne, amma ya na jin tsoron fara yin shuka, saboda jinkirin na saukar Ruwan sama, inda ya sanar da cewa, ya na jin tsoro idan ya yi shukar a yuanzu, saboda jinkirin saukar Ruwan saman, zai iya yin asara.
A cewar Echioda, jinkirin na saukar Ruwan saman ya kuma dakatar da shi daga yunkurinsa na saon shuka sauran amfanin gona, kamar su Masara da sauransu.
“Jinkirin na saukar Ruwan saman ya kuma dakatar da shi daga yunkurinsa na saon shuka sauran amfanin gona, kamar su Masara da sauransu.”
Bugu da kari, wasu manoman a garin Gboko da ke a cikin jihar ta Biniwe, suma sun koka kan samun jinkirin na sauikar Ruwan sama.
Sai dai, wasu daga cikin namoman a garin na Gboko sun bayyana cewa, sun kasada sun yi shuka a gonakan su, amma suna jin tsoron fuskantar asara.