Shugaban kasar Congo Kinshasa Felix Tshisekedi, ya bayyana cewa, ya cimma nasara a ziyarar da ya gudanar a kasar Sin a kwanakin baya, wadda ta kara imanin kasarsa a fannin inganta hadin gwiwa da sada zumunta da kasar Sin.
Shugaba Tshisekedi ya bayyana hakan ne yayin da sabon jakadan Sin a kasar ta Congo Kinshasa Zhao Bin, ya mika masa takardar kama aiki a fadar sa, inda shugaban ya ce ba zai manta da nasarar ziyararsa a kasar Sin ba. Ya ce ziyarar ta karawa Congo Kinshasa sanin kasar Sin, da kara imaninta ga inganta hadin gwiwa, da sada zumunta a tsakanin kasashen biyu.
Shugaban na Congo Kinshasa, ya ce zai ci gaba da yin kokari tare da kasar Sin, wajen aiwatar da ayyukan da aka cimma matsaya a kan su yayin ziyarar ta sa, da daga matsayin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki.
A nasa bangare, jakada Zhao Bin ya bayyana cewa, a yayin ziyarar shugaba Tshisekedi, shugabannin kasashen Sin da Congo Kinshasa, sun inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, zuwa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, kana an tsara taswirar raya dangantakarsu.
Zhao Bin ya ce, yana fatan yin kokari tare da bangaren kasar Congo Kinshasa, wajen aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka cimma daidaito a kai, da inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki. (Zainab)