Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya rantsar da Mai Shari’a Olukayode Ariwoola a matsayin Alkalin Alkalai na Kasa (CJN) na wucin gadi, bayan murabus din Mai Shari’a Tanko Muhammad da safiyar ranar Litinin.
Mai Shari’a Tanko, ya yi murabus daga mukaminsa ne bisa rahoton rashin lafiya, a cewar wata sanarwa da mataimaki na musamman na shi kan harkokin yada labarai, Isah Ahuraka ya fitar.
- Amurka Na Shirin Bai Wa Ukraine Makami Mai Linzami Don Yakar Rasha
- 2023: An Bukaci INEC Ta Dakatar Da Tinubu Kan Zargin Rashin Takardun Karatu
Wannan dai na zuwa ne biyo bayan tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa da kuma sauran laifuka a kan da ‘yan uwansa alkalan kotun koli 14 suke yi masa.
Ariwoola, wanda ya isa zauren majalisar tare da takwarorinsa alkalan kotun koli da misalin karfe 2:45 na rana a cikin wata farar bas mai launin fari, inda za a rantsar da shi.
An rawaito cewa Ariwoola, shi ne mafi girman mukami bayan mai shari’a Mary Odili da ta yi ritaya a ranar 12 ga watan Mayu 2022, bayan ta cika shekara 70 a duniya.
Shi ma Ariwoola, a 2028 a ke sa ran zai yi ritaya daga aiki.
An nada Mai Shari’a Olukayode Ariwoola, a matsayin Alkalin Kotun Kolin Nijeriya a 2011.