Bisa rahoton da kungiyar masana’antun kera motoci ta kasar Sin ta fidda, an ce, a watan Mayu, adadin motocin da aka samar a kasar Sin ya kai guda miliyan 2 da dubu 333, adadin da ya karu da kashi 21.1 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. A sa’i daya kuma, adadin motocin da aka sayar a wannan wata ya kai miliyan 2 da dubu 382, wanda ya karu da kashi 27.9 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.
Haka kuma, adadin motoci masu amfani da wutar lantarki da aka samar a watan Mayu ya kai dubu 713, adadin ya karu da kashi 53 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara, kana, adadin motoci masu amfani da wutar lantarki da aka sayar ya kai dubu 717, wanda ya karu da kashi 60.2 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kana, yawan motoci masu aiki da wutar lantarki dake cikin kasuwanni ya kai kashi 30.1 bisa dari.
Game da batun motocin da aka sayar zuwa ketare kuma, a watan Mayu, an sayar da motoci guda dubu 389 zuwa ketare, adadin ya karu da kashi 58.7 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. (Mai Fassrawa: Maryam Yang)