Hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ta ce bayar da biza 73,310 daga cikin kujeru 75,000 da aka ware wa jihohi domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023.
Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Shugaban Hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan ya bayyana cewa hukumar ta kwashe maniyyata 46,258 zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana tun daga ranar 25 ga watan Mayu da aka fara jigilar maniyyata.
- Kungiya Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Kan Inganta Tsaro Da Yaki Da Rashawa
- Hikimar Kasar Sin Ta Ba Da Gudummuwa Ga Ci Gaban Kungiyar SCO
Shugaban hukumar wanda ya samu wakilcin Kwamishinan NAHCON na bangaren tsare-tsare, Bincike, kididdiga, watsa labarai da ayyukan dakin karatu, Sheikh Suleiman Momoh ya bayyana cewa duk da wasu kalubale da ake fuskanta a lokacin aikin jigilar maniyyata, hukumar ba za ta bar kowa daga cikin maniyyatan da suka yi rajista ba.
“Akwai wasu kalubale da muke fuskanta saboda lalacewar na’urorin, amma muna himma don tabbatar da cewa duk wani yanayi da ya faru za mu dauki matakin gaggawa wajen shawo kan lamarin tare da mayar da abubuwa yadda suke.”
Ya kara da cewa, an tanadi masauki da ciyarwa da mahajjata mai kyau a Madina, yayin da hukumar ke tabbatar da cewa dukkan majiyyata sun gudanar da ibadarsu yadda ya dace a can.
Ya kuma bayyana cewa a karon farko kasar ta cika dukkan rarar da aka bai wa hukumar sakamakon koma-bayan da maniyyatan suka samu lokacin cutar Karona.
Ya ce yayin da ya rage na makwanni biyu a fara aikin hajji, hukumar za ta tabbatar da cewa dukkan maniyyatan suna kasar Saudiyya kafin lokaci ya kure.
“Muna duban wuraren da aka samu nasara da kuma wanda aka samu nakasu, amma muna tabbatar da cewa babu wani maniyyaci da ya yi rajista da ba za a kai shi kasa mai tsarki ba kafin wa’adi ya kare,” in ji shi.