Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake saduwa da ku a wannan makon a cikin shirin na mu na girki ado mata.
Uwargida idan kina son ki burge maigida da hadeddan lemo ba sai kin je shago ba da kanki za ki hada lemon da zai kayatar da maigida:
- Hajjin Bana: NAHCON Ta Samar Da Biza 73,310, Tare Da Kai Alhazai 46,000 Kasar Saudiyya
- Zan Yi Aiki A Bayyane Tare Da Shugabannin Majalisa Ta 10 – Tinubu
Abubuwa da ya kamata uwargida ki tanada:
Tuffa, Abarba, kokumba, danyar citta, suga, lemon kwali dan kadan haka blender:
Yadda uwargida za ki hada lemonki:
Da farko za wanke tuffarki sai ki yayyanka ta ki ajiye ta a gefe, sannan abarba ki wanke ta sai ki fere bayan sannan ki yayyanka ta kanana itama ki ajiye a gefe, sannan kokumba itama ki wanke ta wajan wanki ki dan sa mata gishiri itama ki yayyanka ta, sai ki dakko blender ki zuba tuffar ki zuba abarbar tare da kokumba.
Sannan ki wanke danyar cittarki ‘yaddai dai haka ki zuba sai ki dan sa ruwa dan daidai yadda lemon zai dan yi kauri kar ya salance, sai ki yi blending din su gaba daya ya yi laushi so sai saboda tace shi za ki yi idan ya yi laushi sai ki samu rariya ki tace shi so sai ki matse sannan ki zuba suga sai ki zuba dan lemon ki mai dadi amma idan kina da lemon bawo mai daki tou tun kafin ki yi blending din za ki gyara shi ki yayyanka shi sai ki zuba su tare to ba sai kin samo lemon kwali ba idan kin sa na bawo. Asha dadi lafiya.