Wasu daga cikin manoma a jihar Katsina sun bayyana jin dadinsu akan furucin gwamnan jihar Dikko Umar Radda na farfado da fannin aikin noma da kuma kara habaka fannin tattalin arzikin jihar.
Manoma sun bayyana jin dadin na su ne, biyo bayan jawabin da Radda ya yi bayan a rantsar da shi a matsayin sabon gwamnan jihar a watan da ya wuce.
- Hajjin Bana: NAHCON Ta Samar Da Biza 73,310, Tare Da Kai Alhazai 46,000 Kasar Saudiyya
- Kungiya Ta Yaba Wa Shugaba Tinubu Kan Inganta Tsaro Da Yaki Da Rashawa
Radda, a jawabin na sa ya bara tabbacin cewa, gwamnatinsa za ta tabbatar da ta zuba jari a fannin, wanda hakan zai sa manoman jihar su samu ribar da ta kai ta sama da kashi 85.
Bugu da kari, ya kuma yi alkawarin kara bunkasa fannin tattalin arzikin jihar.
Daya daga cikin manoman da ke noman Masara Alhaji Wada Isah a karamar hukumar Dandume ya bayyana cewa, ya kamata gwamntin jihar ta janyo manoman jihar wajen wanzar da tsare-tsare da kuma shirye-shiryen da ta zo da su don a samu nasara wajen habaka fanin.
Sun yi nuni da cewa, ganin cewa Radda shi ma manomi ne da kuma irin kokarin da ya yi a lokacin da yake rike da shugabancin hukuar SMEDAN, muna da yakinin cewa, zai iya samar da sauyi a fannin aikin noman jihar.
“Ya kamata gwamntin jihar ta janyo manoman jihar wajen wanzar da tsare-tsare da kuma shirye-shiryen da ta zo da su don a samu nasara wajen habaka fanin.”
Ya sanar da cewa, babban abinda ya fi ci masu Tuwo a Kwarya shine tsadar Takin zamani, magungunan feshi da sauransu.
Shi ma wani manomin da ke a karamar hukumar Faskari Habibu Garba ya bayyana cewa, kara habaka yin noma don samun riba, musaman noman Waken Soya, Alkama da kuma Masar, hakan zai kara habaka fannin aikin noma na jihar da kuma kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasa.
A cewar Habibu, samar wa da moman jihar rumbun adana amfanin noma da suka girbe, musamman Tumatir da Albasa, Dankalin turawa, musamman don su rage asarar da suke yi .
“Kara habaka yin noma don samun riba, musaman noman Waken Soya, Alkama da kuma Masar, hakan zai kara habaka fannin aikin noma na jihar da kuma kara samar da ayyukan yi, musamman a tsakanin matasa.”
Habibu ya kara cewa, manoman sun shafe shekaru da dama suna burin a samar masu da Rubun adana amfanin gonakansu da suka noma.
Ya sanar da kara fadada noman Dankalin turawa a jihar, musamman a karamar hukumar Bakori na da banna mahimmanci ba a karamar hukumar kawai ba, har da a fadin jihar .
“Manoman sun shafe shekaru da dama suna burin a samar masu da Rubun adana amfanin gonakansu da suka noma.”