Jagora a yankin Niger Delta, Asari Dokubo, ya bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da kada ya saki shugaban haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu.
Dokubo wanda ke tattauna da ‘yan jarida bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Villa Abuja ranar Juma’a.
- Kungiyoyin Arewa Sun Yi Fatali Da Bukatar Sakin Nnamdi Kanu
- Ohanaeze Ta Bukaci Tinubu Ya Saki Nnamdi Kanu Idan Aka Rantsar Da Shi
Jagoran Niger Delta, ya ce, sakin Kanu tamkar farfado ayyukan ci gaba da kashe mutane da aikace-aikacen ta’addanci ne, kuma hakan zai zama tamkar tukuici ne ga laifukan da ya aikata, ya ce, kamatuwa ya yi Kanu ya fuskanci shari’a.
Idan za a tuna, tun lokacin da aka sake kama Kanu a 2021 yake tsare a hannun hukumar DSS inda ke fuskantar shari’ar zargin ta’addanci.
A shekarar 2017 ne kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin Kanu amma ya karya ka’idojin belinsa lamarin da ya sanya shi arcewa daga Nijeriya zuwa kasar waje, sannu a hankali kuma jami’an tsaro suka sake kamo shi.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sha matsin lamba na bukatar ya sake Kanu amma ya yi mursisi, inda a yanzu bayan kafa sabuwar gwamnati wasu da dama suke ta sabunta kiran a sake shugaban na IPOB.
Da yake magana kan tsare Kanu, Asari Dokubo ya ce, “Sakin Nnamdi Kanu tamkar biyan tukuici ne ga ayyukan ta’addanci da kisan rayukan wadanda ba su ji ba su gani ba.”
Ya kara da cewa, “Kamatuwa ya yi kawai ya fuskanci shari’a kan ayyukansa da laifukan da ya aikata.” Cewar Dokubo.