Inuwar gamayyar masu ruwa da tsaki a kan ilimi a Jihar Kano sun nuna goyon bayansu na kwato muhallan makarantu da gwamnatin mai ci yanzu ta ke yi.
Dakta Ibrahim Usman Aikawa ne, ya bayyana haka a taron manema labarai da suka gudanar a ranar Talata.
Ya ce taron nasu na wayarwa da mutane kai ne, a kan martabar da darajar ilimi da nuna goyon baya ga matakai da gwamnati a Jihar Kano ta dauka a kan filayen makarantu da ake karbowa.
Ya yi nuni da cewa suna sane da cewa wasu za su samu rashin jindadi a kan abin da yake faruwa amma wannan abu an yi shi ne don ci gaban al’umma domin magabata sun san martaba na ilimin Addinin dana boko saboda daraja da girmama ilimi Manzon Allah ya yi umarni aje a nemi ilimi ko a birnin Sin ne.
Dakta Aikawa, ya ce “marigayi Nelson Mandela na Afirka ta Kudu, ya ce ilimi ne makami da za ka yi amfani da shi da za ka iya juya duniya ta abin da kake so, amma a wannan yanayin ne aka samu wasu marasa kishi da rashin kaunar ci gaban ilimi a Kano suka handame filayen makarantu suka mayar da su gidaje da shaguna da wajen taron biki da wasanni.”
Ya ce duk wanda ya yi korafi a kan an rushe masa gida cewa yake a filin Salanta, ba sa cewa a filin makarantar Kano Poly saboda sanin idan suka fadi haka kowa zai gane sun shiga harkar filin ne.
Ya ce akwai wanda ya ce ya kashe miliyan 800 a gininsa duk wanda zai iya kashe irin wannan kudi ya gina gida da wuya a samu iyalansa na zuwa makarantun gwamnati sai wanda zai biya ko ba a kasar nan ba su yi karatu, amma ya zo ya debi kayan talakawa ya yi gini a kai saboda ana so a mallake ‘yancin talaka a hana ‘ya’yansu ilimi.
Aikawa, ya yi kira ga Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a kan ya ci gaba da daukar matakai irin wadannan na rushe gini da aka yi ba bisa ka’ida ba, a kan zalunci don rusa ilimi a Jihar Kano.
Ya kara da cewa ya kamata a dauki tsauraran matakai na yin dokoki don hana wani nan gaba ya sake sayar da wajen makarantu na al’umma.